Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Dabarun Jan Hankali A Waƙoƙin Baka: Nazari A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi

View through CrossRef
Tsakure Waƙoƙin baka na Hausa cike suke da dabarun jawo hankali. Wannan ya sa a kodayaushe za a ga waƙoƙin suna cike da armashi da salo mai ban-sha'awa. Gusau (2003 da 2023) ya kira waɗannan dabaru da adon harshe. Ɗangambo (2007) yana ambaci waɗannan dabaru da dabarun salon sarrafawa. Abba da Zulyadaini (2011) sun kira su da dabarun fitar da salo. Haka kuma Auta (2017) ya kira su da dabarun jawo hankali. Ashe kenan, dabarun jawo hankali wani reshe na salo da makaɗan baka na Hausa suke amfani da shi wajen isar da saƙonni iri daban-daban a cikin waƙoƙinsu. Babbar manufar wannan takarda ita ce yin nazarin dabarun jawo hankali na kwatantawa da jinsintarwa da siffantawa da kuma alamtarwa a cikin Ɗiyan wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi. An ɗora wannan takarda a kan ra'in Waƙar Baka Bahaushiya na Gusau (2003, 2014 da 2023). An yi amfani da dabarar bincike bi-bayani wajen fito tare da sharhantar ɗiyan waƙoƙi masu ƙunshe da wannan salo ma dabarun jawo hankali. Takardar ta gano cewa Kassu Zurmi ya fi yin amfani da dabarar mutuntarwa a cikin waƙoƙinsa sama da kowace dabara ta jawo hankalin mai sauraron. Fitilun Kalmomi: Dabarun Jaho Hankali, Waƙa, Kassu Zurmi
Title: Dabarun Jan Hankali A Waƙoƙin Baka: Nazari A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Tsakure Waƙoƙin baka na Hausa cike suke da dabarun jawo hankali.
Wannan ya sa a kodayaushe za a ga waƙoƙin suna cike da armashi da salo mai ban-sha'awa.
Gusau (2003 da 2023) ya kira waɗannan dabaru da adon harshe.
Ɗangambo (2007) yana ambaci waɗannan dabaru da dabarun salon sarrafawa.
Abba da Zulyadaini (2011) sun kira su da dabarun fitar da salo.
Haka kuma Auta (2017) ya kira su da dabarun jawo hankali.
Ashe kenan, dabarun jawo hankali wani reshe na salo da makaɗan baka na Hausa suke amfani da shi wajen isar da saƙonni iri daban-daban a cikin waƙoƙinsu.
Babbar manufar wannan takarda ita ce yin nazarin dabarun jawo hankali na kwatantawa da jinsintarwa da siffantawa da kuma alamtarwa a cikin Ɗiyan wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi.
An ɗora wannan takarda a kan ra'in Waƙar Baka Bahaushiya na Gusau (2003, 2014 da 2023).
An yi amfani da dabarar bincike bi-bayani wajen fito tare da sharhantar ɗiyan waƙoƙi masu ƙunshe da wannan salo ma dabarun jawo hankali.
Takardar ta gano cewa Kassu Zurmi ya fi yin amfani da dabarar mutuntarwa a cikin waƙoƙinsa sama da kowace dabara ta jawo hankalin mai sauraron.
Fitilun Kalmomi: Dabarun Jaho Hankali, Waƙa, Kassu Zurmi.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi...

Back to Top