Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi

View through CrossRef
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zamantakewar al’ummar Hausawa. Haka kuma, an yi amfani da hanyar nazarin waƙar baka Bahaushiya, wato (Gusau,2023) domin yin gajoranci wajen ƙalailece misalan wannan nazarin. Har ila yau, hanyoyin da aka yi amfani da su a wajen tattaro bayanai da misalan ɗiyan waƙoƙin da aka yi amfani da su, sun haɗa da sauraren wasu waƙoƙin kai tsaye a MP3 sannan aka juyar da su a rubuce kuma tsamo wasu ɗiyan waƙoƙin daga Diwanin Waƙoƙin baka na Hausa (Gusau, 2009 da 2014), da kuma littafi mai ɗauke da waƙoƙin Kassu Zurmi, wato (Magaji, 2016) da Kundin Ƙaura (2017). Har wa yau, an yi amfani da hanyar bi-sharhi, wato (}ualitative Research). A wannan takarda an fahimce, Kassu Zurmi yana amfani da dabarun na bibiyar yanayin dangantakar masu sarauta da ‘yantauri a tsarin zamantakewar al’umma Hauswa, musamman a kan abin da ya shafi gudanar da mulki irin na sarauta a kowa ne mataki. Har ila yau, an lura, a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi an nuna yadda kyakkyawar dangantaka take tsanin masu sarauta da ‘yantauri, musamman ta fuskar samar da tsaro da kuma bayar da kariya ga masarauta da masu sarauta da kuma tabbatar da hukunci. Sannan kuma an lura ‘yantauri mutane masu nuna jajircewa da juriya da kuma kuri don tsoratarwa. Wanda hakan ta sa kusan kowane mai sarauta, musamman mai gunduma yake da sarkin tauri.
Title: Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Description:
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zamantakewar al’ummar Hausawa.
Haka kuma, an yi amfani da hanyar nazarin waƙar baka Bahaushiya, wato (Gusau,2023) domin yin gajoranci wajen ƙalailece misalan wannan nazarin.
Har ila yau, hanyoyin da aka yi amfani da su a wajen tattaro bayanai da misalan ɗiyan waƙoƙin da aka yi amfani da su, sun haɗa da sauraren wasu waƙoƙin kai tsaye a MP3 sannan aka juyar da su a rubuce kuma tsamo wasu ɗiyan waƙoƙin daga Diwanin Waƙoƙin baka na Hausa (Gusau, 2009 da 2014), da kuma littafi mai ɗauke da waƙoƙin Kassu Zurmi, wato (Magaji, 2016) da Kundin Ƙaura (2017).
Har wa yau, an yi amfani da hanyar bi-sharhi, wato (}ualitative Research).
A wannan takarda an fahimce, Kassu Zurmi yana amfani da dabarun na bibiyar yanayin dangantakar masu sarauta da ‘yantauri a tsarin zamantakewar al’umma Hauswa, musamman a kan abin da ya shafi gudanar da mulki irin na sarauta a kowa ne mataki.
Har ila yau, an lura, a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi an nuna yadda kyakkyawar dangantaka take tsanin masu sarauta da ‘yantauri, musamman ta fuskar samar da tsaro da kuma bayar da kariya ga masarauta da masu sarauta da kuma tabbatar da hukunci.
Sannan kuma an lura ‘yantauri mutane masu nuna jajircewa da juriya da kuma kuri don tsoratarwa.
Wanda hakan ta sa kusan kowane mai sarauta, musamman mai gunduma yake da sarkin tauri.

Related Results

Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Al’adun kyautata zamantakewa, al’adu ne masu ɗimbin yawa da har yau ba a ƙayyade su ba, da ma dai al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Don haka dukkan tsarin da al’ad...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...

Back to Top