Javascript must be enabled to continue!
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi. Binciken ya waiwayi ayyukan magabata waɗanda suke da alaƙa da nazarin. Wasu daga cikin hanyoyin tattara bayanan da aka yi amfani da su sun haɗa da: Sauraren waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da gudanar da hira ko tattaunawa da waɗanda suke da masaniya game da nazarin da aka gudanar, sai kuma karance-karance. Maƙalar ta yi amfani da tunanin Bahaushe da ke cewa: “Akwai ruwa a ƙasa, sai ga wanda bai tona ba” a matsayin hanyar ɗora aiki. Wasu daga cikin sakamakon da aka gano sun haɗa da: Hausawa suna da tsarin lokacinsu tun kafin su cuɗanya da wasu al’ummu. Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi suna ƙunshe da al’adun Hausawa waɗanda suka shafi zamantakewarsu da kuma yanayin yadda suke amfani da lokatai. Haka kuma, Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi ya yi amfani da lokatan damina da na rani a waƙoƙinsa domin nuna matsayinsu da kuma tasirinsu a rayuwar Hausawa. Keɓaɓɓun Kalmomi: Lokuta da Gargajiya da kuma Baki.
Title: Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Description:
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi.
Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi.
Binciken ya waiwayi ayyukan magabata waɗanda suke da alaƙa da nazarin.
Wasu daga cikin hanyoyin tattara bayanan da aka yi amfani da su sun haɗa da: Sauraren waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da gudanar da hira ko tattaunawa da waɗanda suke da masaniya game da nazarin da aka gudanar, sai kuma karance-karance.
Maƙalar ta yi amfani da tunanin Bahaushe da ke cewa: “Akwai ruwa a ƙasa, sai ga wanda bai tona ba” a matsayin hanyar ɗora aiki.
Wasu daga cikin sakamakon da aka gano sun haɗa da: Hausawa suna da tsarin lokacinsu tun kafin su cuɗanya da wasu al’ummu.
Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi suna ƙunshe da al’adun Hausawa waɗanda suka shafi zamantakewarsu da kuma yanayin yadda suke amfani da lokatai.
Haka kuma, Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi ya yi amfani da lokatan damina da na rani a waƙoƙinsa domin nuna matsayinsu da kuma tasirinsu a rayuwar Hausawa.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Lokuta da Gargajiya da kuma Baki.
Related Results
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Duk wani abu da ya shafi fasahar bayyana nagartaccen tsarin rayuwa ta mutum da kuma al’umma wadda ta shafi duniya da wadda ta shafi Lahira tana nan tule a cikin waƙoƙin baka na Hau...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ...

