Javascript must be enabled to continue!
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masana harshe sun aminta cewa kalmomin sunaye a kowane harshe suna da ma’ana kuma akwai ra’in da ake nazarin sunaye ta la’akari da asalinsu ko tarihinsu ko kuma yadda suka bayyana tare da sauye-sauyen da suke samu. Wannan maƙala mai taken: Nazarin Sunaye a cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi ta yi fito da wasu sunayen da marigayi Alhaji Kassu Zurmi ya yi amfani da su a cikin wasu waƙokinsa guda goma sha ɗaya da aka yi nazari. Manufar maƙalar ita ce nazarin waɗannan sunayen a bisa faifan nazarin sunaye a fagen ilimin kimiyyar harshe (onomastics) wanda yake nazarin kalmomin sunaye da kuma rarraba su ta la’akari da asali da tarihi da kuma yadda aka samar da su. An yi amfani da wannan ra’in ne wajen nazarin rukunin sunaye na wurare da ɗaiɗaikun mutanen da Kassu Zurmi ya yi amfani da su a cikin waƙoƙin. Binciken ya yi amfani da dabarun bincike na sauraren waƙoƙin da kuma karanta wasu matanin waƙoƙin Kassu Zurmi da aka rubuta wajen tsamo irin waɗannan sunayen da kuma rarraba su a cikin rukunan da aka same su kamar yadda wannan ra’in ya tanada. Bimciken ya taƙaita ne kawai ga nazarin waƙoƙi goma sa ɗaya (11) na Kassu Zurmi da suka ƙunshi waƙoƙin tauri da waƙoƙin farauta da waƙoƙin ɓarayi inda aka fito da adadin sunayen guda ɗari biyu da bakwai (207) da suka haɗa da sunayen wurare (garuruwa da ƙauyuka) da sunayen ɗaiɗakun mutane da aka rarraba a cikin rukunin; sunayen yanka da sunayen laƙabin dangantaka da sunayen gargajiya da sunayen sarauta da kuma sunayen jaruntaka ko kirari. Daga waɗannan sunayen da aka samu binciken ya tabbatar muna da fahimtar mafi yawan duniyar da marigayi Kassu Zurmi ya rayu a cikinta da kuma inda ya yi waƙoƙinsa a lokacin rayuwarsa da mutanen da ya yi wa waƙoƙin musamman kasancewar wasu sunayen da an ji su ko da ba a cikin waƙoƙinsa ba ne wanda ya saba sauraren waƙoƙin zai iya tunawa da lalle wannan suna fitacce ne a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi.
Sokoto State University
Title: Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani.
Masana harshe sun aminta cewa kalmomin sunaye a kowane harshe suna da ma’ana kuma akwai ra’in da ake nazarin sunaye ta la’akari da asalinsu ko tarihinsu ko kuma yadda suka bayyana tare da sauye-sauyen da suke samu.
Wannan maƙala mai taken: Nazarin Sunaye a cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi ta yi fito da wasu sunayen da marigayi Alhaji Kassu Zurmi ya yi amfani da su a cikin wasu waƙokinsa guda goma sha ɗaya da aka yi nazari.
Manufar maƙalar ita ce nazarin waɗannan sunayen a bisa faifan nazarin sunaye a fagen ilimin kimiyyar harshe (onomastics) wanda yake nazarin kalmomin sunaye da kuma rarraba su ta la’akari da asali da tarihi da kuma yadda aka samar da su.
An yi amfani da wannan ra’in ne wajen nazarin rukunin sunaye na wurare da ɗaiɗaikun mutanen da Kassu Zurmi ya yi amfani da su a cikin waƙoƙin.
Binciken ya yi amfani da dabarun bincike na sauraren waƙoƙin da kuma karanta wasu matanin waƙoƙin Kassu Zurmi da aka rubuta wajen tsamo irin waɗannan sunayen da kuma rarraba su a cikin rukunan da aka same su kamar yadda wannan ra’in ya tanada.
Bimciken ya taƙaita ne kawai ga nazarin waƙoƙi goma sa ɗaya (11) na Kassu Zurmi da suka ƙunshi waƙoƙin tauri da waƙoƙin farauta da waƙoƙin ɓarayi inda aka fito da adadin sunayen guda ɗari biyu da bakwai (207) da suka haɗa da sunayen wurare (garuruwa da ƙauyuka) da sunayen ɗaiɗakun mutane da aka rarraba a cikin rukunin; sunayen yanka da sunayen laƙabin dangantaka da sunayen gargajiya da sunayen sarauta da kuma sunayen jaruntaka ko kirari.
Daga waɗannan sunayen da aka samu binciken ya tabbatar muna da fahimtar mafi yawan duniyar da marigayi Kassu Zurmi ya rayu a cikinta da kuma inda ya yi waƙoƙinsa a lokacin rayuwarsa da mutanen da ya yi wa waƙoƙin musamman kasancewar wasu sunayen da an ji su ko da ba a cikin waƙoƙinsa ba ne wanda ya saba sauraren waƙoƙin zai iya tunawa da lalle wannan suna fitacce ne a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi.
Related Results
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi...

