Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi

View through CrossRef
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunawa tsakanin makaɗi da masu sauraro ko da tauraro ko kuma da wasu a cikin waƙa dangane da wata matsala ko wani sha’ani da waƙa ta ƙunsa. Maƙalar ta nazarci salon hira da ke cikin waƙoƙin biyu, an kuma sami wasu nau’o’in salon hira da makaɗin ya yi amfani da su a cikin waƙoƙin nasa kamar yadda ƙumshiyar takardar ta bayyana. An yi haka ta fuskar farauto waƙoƙin da sauraren su da yin nazarin su, aka saurare su da kuma tsamo salon hira a cikinsu. Maƙalar ta gano cewa, akwai nau’o’in salon hira daban-daban a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi, kuma an kawo su ɗaya bayan ɗaya tare da bayani da ingantatun misalai. An kawo misali na kowane nau’in salo da aka samu daga waƙoƙin da aka nazarta. Haka kuma, maƙalar ta gano cewa makaɗa Kassu haziƙi ne a fagen waƙa, kuma shi kaɗai ke rera waƙoƙinsa ba tare da taimakon ‘yan amshi ba. Daga cikin nazarin da aka yi, maƙalar ta gano cewa salon hira muhimmi ne a cikin waƙoƙin baka domin yana ƙayatarwa sosai tare da jan hankulan masu sauraro dangane da abubuwan da suke gudana tsakanin jama’a a cikin waƙa.Kadadar wannan maƙala ita ce waƙoƙin biyu da aka zaɓa, wato, waƙar Nomau Namagarya da waƙar Shayi ɗan Gidan Labbo.
Title: Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Description:
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai.
Salon hira na nufin tattaunawa tsakanin makaɗi da masu sauraro ko da tauraro ko kuma da wasu a cikin waƙa dangane da wata matsala ko wani sha’ani da waƙa ta ƙunsa.
Maƙalar ta nazarci salon hira da ke cikin waƙoƙin biyu, an kuma sami wasu nau’o’in salon hira da makaɗin ya yi amfani da su a cikin waƙoƙin nasa kamar yadda ƙumshiyar takardar ta bayyana.
An yi haka ta fuskar farauto waƙoƙin da sauraren su da yin nazarin su, aka saurare su da kuma tsamo salon hira a cikinsu.
Maƙalar ta gano cewa, akwai nau’o’in salon hira daban-daban a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi, kuma an kawo su ɗaya bayan ɗaya tare da bayani da ingantatun misalai.
An kawo misali na kowane nau’in salo da aka samu daga waƙoƙin da aka nazarta.
Haka kuma, maƙalar ta gano cewa makaɗa Kassu haziƙi ne a fagen waƙa, kuma shi kaɗai ke rera waƙoƙinsa ba tare da taimakon ‘yan amshi ba.
Daga cikin nazarin da aka yi, maƙalar ta gano cewa salon hira muhimmi ne a cikin waƙoƙin baka domin yana ƙayatarwa sosai tare da jan hankulan masu sauraro dangane da abubuwan da suke gudana tsakanin jama’a a cikin waƙa.
Kadadar wannan maƙala ita ce waƙoƙin biyu da aka zaɓa, wato, waƙar Nomau Namagarya da waƙar Shayi ɗan Gidan Labbo.

Related Results

Nazarin Neman Auren Hausawa a Cikin Waƙar Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi Ta Shayi Ɗan Gidan Labbo
Nazarin Neman Auren Hausawa a Cikin Waƙar Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi Ta Shayi Ɗan Gidan Labbo
Wannan maƙala ta yi nazarin neman auren Hausawa a cikin waƙar Makaɗa Abubakar Kassu Zurni ta Shayi ɗan gidan Labbo. Manufar wannan maƙala ita ce, fito da wasu al’adun neman aure, ...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
NAZARIN YALWAR MA’ANAR KALMOMI A CIKIN WAƘOƘIN KASSU ZURMI
NAZARIN YALWAR MA’ANAR KALMOMI A CIKIN WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Wannan takardar za ta mayar da hankali ne kan ilimin ma’anar kalmomi waɗannda suka shafi yalwar ma’ana a cikin waƙoƙi biyu na Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, waƙar Nomau na Magarya da...
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi...
Gurbin Musulunci A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Gurbin Musulunci A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙan Hausa mutane ne da Allah ya yi wa baiwa da basira da hikimomi wajen tsara zantuttukan hikima a cikin baitocin waƙa ko ɗiyan waƙa. Wannan baiwa da Allah ya yi musu ya sa ake...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...

Back to Top