Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi

View through CrossRef
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi rukunin masu fama da nakasar kisan-raɓa a waƙoƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa ‘yan taurinsa. Nazarin ya mayar da hankali ga waƙar Shayi ɗan gidan Labbo a matsayin karan bara. Domin yi wa binciken adalci, an waiwayi ayyukan magabata wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba. Wasu daga cikin hanyoyin tattara bayanan da aka yi amfani da su sun haɗa da: Sauraren waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da gudanar da hira ko tattaunawa da waɗanda suke da masaniya game da nazarin da aka gudanar, sai kuma karance-karance. Maƙalar ta yi amfani da tunanin Bahaushe (karin magana) da ke cewa: “Maƙwabcin mai kanwa ba ya rasa ɗan ɓarɓashi” a matsayin hanyar ɗora aiki. Wasu daga cikin sakamakon da nazarin ya gano sun haɗa da: Nakasar kisan-raɓa ɗaya ce daga cikin larurorin da suke addabar wasu mutane. Har wa yau, kisan–raɓa nakasa ce da ta shafi mutuwar zuciya, don haka ba a ganin ta ƙuru-ƙuru da ido, sai dai ayyukan wanda ta kama su nuna. Bugu da ƙari, Kisan-raɓa nakasa ce da takan riski wasu a dalilin sakaci, wasu kuma ƙaddara ce ta riga fata. Daga cikin shawarwarin da takardar ta gano sun haɗa da, akwai buƙatar al’umma su sanya wa kansu kishin kai, ta yadda kowa zai tashi ya nemi na kansa kamar yadda magabatanmu suka gudanar da rayuwarsu. Haka kuma, sanya yara a tafarkin jin daɗi, wani abu ne da zai ci gaba da haifar da wannan larura. Domin ko ba komai, idan muka tuna magabata, masu larurar makanta da gurgunta duka suna tashi tsaye su yi sana’a domin samar wa kansu mafita. Keɓaɓɓun Kalmomi: Halaye da Kisan-raɓa da kuma ‘Yan Tauri
Title: Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Description:
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba.
Wannan takarda ta dubi rukunin masu fama da nakasar kisan-raɓa a waƙoƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa ‘yan taurinsa.
Nazarin ya mayar da hankali ga waƙar Shayi ɗan gidan Labbo a matsayin karan bara.
Domin yi wa binciken adalci, an waiwayi ayyukan magabata wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba.
Wasu daga cikin hanyoyin tattara bayanan da aka yi amfani da su sun haɗa da: Sauraren waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da gudanar da hira ko tattaunawa da waɗanda suke da masaniya game da nazarin da aka gudanar, sai kuma karance-karance.
Maƙalar ta yi amfani da tunanin Bahaushe (karin magana) da ke cewa: “Maƙwabcin mai kanwa ba ya rasa ɗan ɓarɓashi” a matsayin hanyar ɗora aiki.
Wasu daga cikin sakamakon da nazarin ya gano sun haɗa da: Nakasar kisan-raɓa ɗaya ce daga cikin larurorin da suke addabar wasu mutane.
Har wa yau, kisan–raɓa nakasa ce da ta shafi mutuwar zuciya, don haka ba a ganin ta ƙuru-ƙuru da ido, sai dai ayyukan wanda ta kama su nuna.
Bugu da ƙari, Kisan-raɓa nakasa ce da takan riski wasu a dalilin sakaci, wasu kuma ƙaddara ce ta riga fata.
Daga cikin shawarwarin da takardar ta gano sun haɗa da, akwai buƙatar al’umma su sanya wa kansu kishin kai, ta yadda kowa zai tashi ya nemi na kansa kamar yadda magabatanmu suka gudanar da rayuwarsu.
Haka kuma, sanya yara a tafarkin jin daɗi, wani abu ne da zai ci gaba da haifar da wannan larura.
Domin ko ba komai, idan muka tuna magabata, masu larurar makanta da gurgunta duka suna tashi tsaye su yi sana’a domin samar wa kansu mafita.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Halaye da Kisan-raɓa da kuma ‘Yan Tauri.

Related Results

Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi d...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...

Back to Top