Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi

View through CrossRef
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri a cikin waƙoƙinsa. Takardar an ginata ne ta hanyar nazartar wasu muhimman aiyukan da aka wallafa da waɗanda ba a wallafa ba. Haka kuma an nazarci wasu turakun waƙoƙin da Kassun ya gabatar, musamman waɗanda suke magana a kan Tauri da magungunan Tauri. Ganin cewa Kassu Zurmi ya naƙalci al’adar Tauri ya sa aka ɗora wannan aiki a kan Karin maganar Hausawa da ake cewa “Masu abi su ke da abinsu”. An yi tsokaci ne a kan irin fashin baƙin da Kassun ya yi wa al’adar Tauri acikin sassa guda uku. A sashe na farko an yi tsokaci a kan ma’anar kalmomin da suka haɗa da Tauri da Farfajiya da kuma Tunani tare da bibiyar ire-iren magungunan da ‘yan tauri ke amfani da su, da wasu kalmomi da Kassu ya yi amfani da su a mamadin maganin tauri da kuma yadda ake amfani da magungunan. Sashe na biyu an yi tsokaci ne a kan irin hangen da Kassu ya yi wa al’adar tauri. A sashe na uku an gabatar da shawarwari da ake ganin sun dace. An gabatar da sawarwarin ne ta hanyar tuntuɓar wasu turakun waƙoƙin shi Kassu Zurmi ɗin. Sakamakon da aka samu yayin gina wannan takaarda ya tabbatar da cewa makaɗa Kassu Zurmi ya taskace al’adar tauri kafin rasuwarsa.
Title: Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Description:
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”.
An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri a cikin waƙoƙinsa.
Takardar an ginata ne ta hanyar nazartar wasu muhimman aiyukan da aka wallafa da waɗanda ba a wallafa ba.
Haka kuma an nazarci wasu turakun waƙoƙin da Kassun ya gabatar, musamman waɗanda suke magana a kan Tauri da magungunan Tauri.
Ganin cewa Kassu Zurmi ya naƙalci al’adar Tauri ya sa aka ɗora wannan aiki a kan Karin maganar Hausawa da ake cewa “Masu abi su ke da abinsu”.
An yi tsokaci ne a kan irin fashin baƙin da Kassun ya yi wa al’adar Tauri acikin sassa guda uku.
A sashe na farko an yi tsokaci a kan ma’anar kalmomin da suka haɗa da Tauri da Farfajiya da kuma Tunani tare da bibiyar ire-iren magungunan da ‘yan tauri ke amfani da su, da wasu kalmomi da Kassu ya yi amfani da su a mamadin maganin tauri da kuma yadda ake amfani da magungunan.
Sashe na biyu an yi tsokaci ne a kan irin hangen da Kassu ya yi wa al’adar tauri.
A sashe na uku an gabatar da shawarwari da ake ganin sun dace.
An gabatar da sawarwarin ne ta hanyar tuntuɓar wasu turakun waƙoƙin shi Kassu Zurmi ɗin.
Sakamakon da aka samu yayin gina wannan takaarda ya tabbatar da cewa makaɗa Kassu Zurmi ya taskace al’adar tauri kafin rasuwarsa.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi d...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...

Back to Top