Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi

View through CrossRef
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zamantakewar alaƙar maza da mata tun daga matakin ‘yanmatanci da samartaka har zuwa zamantakewar aure. Hanyoyin da aka yi amfani da su a wajen tattaro bayanai da misalan ɗiyan waƙoƙin da aka yi amfani da su, sun haɗa da sauraren wasu waƙoƙin daga MP3 sannan aka juyar da su a rubuce. Haka kuma an tsamo wasu ɗiyan waƙoƙin daga littattafai masu ɗauke da waƙoƙin Kassu Zurmi. A wannan nazari an lura, Kassu Zurmi yana amfani da dabarun na bibiyar yanayin dangantakar soyayyar da take tsakanin jarumansa da kuma mata duk da cewa yawancin ‘yantauri da mafarauta duk matalauta ne ko kuma matsiyata kamar yadda yake ambatar su a cikin waƙoƙinsa. Har wa yau, an fahimci a wasu waƙoƙin na Kassu Zurmi, yakan nuna yadda kyakkyawar alaƙa take tsakanin mata da maza, musamman ta fuskar yadda ‘yanmata da mata suke nuna gabata da hakin kyauta da rufa asiri da bayar da shawarwari da kuma taimako ga mazajen duk da yanayinsu na fatara. A waƙoƙin na Kassu, an gano cewa, mata suna son mazaje jarumai ko da kuwa ba su da arziki, don shahara ko bajintarsu ko kuma surar jikinsu. Ashe kenan, akwai kyakkyawar alaƙa ta soyayya tsakanin mata da maza jarumai ta hanyar yin haƙuri da yanayinsu na ɗauko magana da kuma rashin yin katabus a ɓangaren hidima, musamman wadda ta shafi kuɗi. Nazarin ya yi ƙoƙarin tabbatar da cewa, waƙoƙin Kassu, waƙoƙi ne da suka yi la’akari da matsayin zamantakewar mace da namiji da tabbatar da tunanin mace ba ta iya yi sai da namiji komai lalacewarsa kamar dai yadda wando ba ya tabbata a ƙugu sai da zariya.
Title: Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Description:
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zamantakewar alaƙar maza da mata tun daga matakin ‘yanmatanci da samartaka har zuwa zamantakewar aure.
Hanyoyin da aka yi amfani da su a wajen tattaro bayanai da misalan ɗiyan waƙoƙin da aka yi amfani da su, sun haɗa da sauraren wasu waƙoƙin daga MP3 sannan aka juyar da su a rubuce.
Haka kuma an tsamo wasu ɗiyan waƙoƙin daga littattafai masu ɗauke da waƙoƙin Kassu Zurmi.
A wannan nazari an lura, Kassu Zurmi yana amfani da dabarun na bibiyar yanayin dangantakar soyayyar da take tsakanin jarumansa da kuma mata duk da cewa yawancin ‘yantauri da mafarauta duk matalauta ne ko kuma matsiyata kamar yadda yake ambatar su a cikin waƙoƙinsa.
Har wa yau, an fahimci a wasu waƙoƙin na Kassu Zurmi, yakan nuna yadda kyakkyawar alaƙa take tsakanin mata da maza, musamman ta fuskar yadda ‘yanmata da mata suke nuna gabata da hakin kyauta da rufa asiri da bayar da shawarwari da kuma taimako ga mazajen duk da yanayinsu na fatara.
A waƙoƙin na Kassu, an gano cewa, mata suna son mazaje jarumai ko da kuwa ba su da arziki, don shahara ko bajintarsu ko kuma surar jikinsu.
Ashe kenan, akwai kyakkyawar alaƙa ta soyayya tsakanin mata da maza jarumai ta hanyar yin haƙuri da yanayinsu na ɗauko magana da kuma rashin yin katabus a ɓangaren hidima, musamman wadda ta shafi kuɗi.
Nazarin ya yi ƙoƙarin tabbatar da cewa, waƙoƙin Kassu, waƙoƙi ne da suka yi la’akari da matsayin zamantakewar mace da namiji da tabbatar da tunanin mace ba ta iya yi sai da namiji komai lalacewarsa kamar dai yadda wando ba ya tabbata a ƙugu sai da zariya.

Related Results

Nazarin Koɗawa da Washi a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Koɗawa da Washi a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar wannan takarda [1] ita ce a aiwatar da nazari kan wasu waƙoƙin Kassu Zurmi yadda yake amfani da tubalin koɗawa da washi wajen gina gundarin saƙo a zubin ɗiyan waƙoƙinsa. An...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi d...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Back to Top