Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Nazarin Koɗawa da Washi a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi

View through CrossRef
Manufar wannan takarda [1] ita ce a aiwatar da nazari kan wasu waƙoƙin Kassu Zurmi yadda yake amfani da tubalin koɗawa da washi wajen gina gundarin saƙo a zubin ɗiyan waƙoƙinsa. An ɗora mizanin tarken wannan takarda ne bisa ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB), wanda Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya assasa (2003, 2008, 2014, 2022, 2024). Sannan kuma, a wannan takarda za a yi amfani da nau’in bincike na bi-bayanin sharhantaka (Descriptive }ualitative Research) wajen fiɗar bayanan bincike. Haka kuma za a yi amfani da tsarin samfuri bi-maƙasudi (Purposive Sampling) wajen zaɓe da juyar waƙoƙin Kassu Zurmi waɗanda suka ɗarsu da tubalin koɗawa da na washi. Kamar yadda Gusau (2022). Saboda haka, wannan takardar za ta yi ƙoƙari wajen tantancewa tare da fayyace yadda Kassu Zurmi ke amfani wajen fito da tunaninsa da gaibiyyarsa cikin hikima da zalaƙar harshe wajen amfani da ƙananan saƙonnin ya koɗa ko kuma ya yi washi ga ɓarayi ko mafarauta ko kuma ‘yantauri a zubin ɗiyan waƙoƙinsa. Za a iya cewa, koɗawa da washi naɗaya daga cikin ginshiƙan ƙananan tubalan da KassuZurmi ke amfani da su wajen sauya tunanin masu sauraron waƙoƙinsa.Domin a mafi yawancin zubin waƙoƙinsa, Kassu Zurmi gwani ne musamman wajen ƙagowa da sauwarawa da kimantawa tare da kuma kwaikwayar haliyya da bajinta da kuma ɗabi’un mafarauta ko `yantauri ko kuma ɓarayi da dai sauransu a zubin ɗiyan waƙoƙinsa.Yana amfani da tubalan koɗawa da na washi ne ya fayyace wani abin arziki, ko bajinta ko waibuwa ko hazaƙa ko wata ɗaukaka da Allah mai girma ya ba wanda yake yi wa waƙa a fagen fama ko na gwajin-sa’a ko na daga ko na yaƙi da dai sauransu. Keɓaɓɓun Kalmomi:Ɓarayi; Koɗawa;Mafarauta; Washi; `Yantauri
Title: Nazarin Koɗawa da Washi a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Manufar wannan takarda [1] ita ce a aiwatar da nazari kan wasu waƙoƙin Kassu Zurmi yadda yake amfani da tubalin koɗawa da washi wajen gina gundarin saƙo a zubin ɗiyan waƙoƙinsa.
An ɗora mizanin tarken wannan takarda ne bisa ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB), wanda Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya assasa (2003, 2008, 2014, 2022, 2024).
Sannan kuma, a wannan takarda za a yi amfani da nau’in bincike na bi-bayanin sharhantaka (Descriptive }ualitative Research) wajen fiɗar bayanan bincike.
Haka kuma za a yi amfani da tsarin samfuri bi-maƙasudi (Purposive Sampling) wajen zaɓe da juyar waƙoƙin Kassu Zurmi waɗanda suka ɗarsu da tubalin koɗawa da na washi.
Kamar yadda Gusau (2022).
Saboda haka, wannan takardar za ta yi ƙoƙari wajen tantancewa tare da fayyace yadda Kassu Zurmi ke amfani wajen fito da tunaninsa da gaibiyyarsa cikin hikima da zalaƙar harshe wajen amfani da ƙananan saƙonnin ya koɗa ko kuma ya yi washi ga ɓarayi ko mafarauta ko kuma ‘yantauri a zubin ɗiyan waƙoƙinsa.
Za a iya cewa, koɗawa da washi naɗaya daga cikin ginshiƙan ƙananan tubalan da KassuZurmi ke amfani da su wajen sauya tunanin masu sauraron waƙoƙinsa.
Domin a mafi yawancin zubin waƙoƙinsa, Kassu Zurmi gwani ne musamman wajen ƙagowa da sauwarawa da kimantawa tare da kuma kwaikwayar haliyya da bajinta da kuma ɗabi’un mafarauta ko `yantauri ko kuma ɓarayi da dai sauransu a zubin ɗiyan waƙoƙinsa.
Yana amfani da tubalan koɗawa da na washi ne ya fayyace wani abin arziki, ko bajinta ko waibuwa ko hazaƙa ko wata ɗaukaka da Allah mai girma ya ba wanda yake yi wa waƙa a fagen fama ko na gwajin-sa’a ko na daga ko na yaƙi da dai sauransu.
Keɓaɓɓun Kalmomi:Ɓarayi; Koɗawa;Mafarauta; Washi; `Yantauri.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...

Back to Top