Javascript must be enabled to continue!
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fagen waƙar baka da fasahar labartawa wajen gudanar da wannan aiki. An ɗora wannan bincike a kan Mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya ta Gusau (2014) Bayan an kammala maƙalar, sai aka gano cewa, da yawa daga cikin ɗiyan waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi da labartawa aka saƙa su. An kuma gano cewa, waƙoƙin Kassu masu fasalin labartawa sun fi tsawo da samun farin jinin masu sauraro. Labartattun ɗiyan waƙa sun fi waɗanda ba labartattun ba yawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi.
Fitilun Kalmomi: Labartawa, waƙa, Kassu Zurmi.
Sokoto State University
Title: Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi.
An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fagen waƙar baka da fasahar labartawa wajen gudanar da wannan aiki.
An ɗora wannan bincike a kan Mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya ta Gusau (2014) Bayan an kammala maƙalar, sai aka gano cewa, da yawa daga cikin ɗiyan waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi da labartawa aka saƙa su.
An kuma gano cewa, waƙoƙin Kassu masu fasalin labartawa sun fi tsawo da samun farin jinin masu sauraro.
Labartattun ɗiyan waƙa sun fi waɗanda ba labartattun ba yawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi.
Fitilun Kalmomi: Labartawa, waƙa, Kassu Zurmi.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...