Javascript must be enabled to continue!
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” maƙala ce da ta yi nazarin ɗaya daga cikin hikimomin da waƙoƙin Kassu Zurmi suka ƙunsa wato kwaikwayon muryoyi daban-daban na mutane da ma wasu sauran halittu. Maƙalar ta yi amfani da waƙoƙi kamar waƙar Nomau Namagarya da waƙar Shayi Ɗangidan Labbo da waƙar Muhammadu Fatake na Dare haka kuma ana iya lalubo misalai daga wasu waƙoƙi masu salo makamancin na Kassu Zurmi. Manufar wannan maƙala ita ce a dubi irin hikimar Kassu wajen kwaikwayo a cikin waƙarsa, sannan a dubi shi kansa kwaikwayon yadda ya rarraba da kuma yadda ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa. Bincike maƙala dai ta jingina ne falsafar waƙe Magana ta Hausawa da ke cewa « Kai kaɗai gayya” da ma dai Kassu Zurmi ba karɓi ake masa ba, saboda haka duk hira da tattaunawar da ka ji cikin waƙoƙinsa duk shi kaɗai ne ke hidimar sa. Abin da binciken wannan maƙala ya gano shi Kassu Zurmi ya yi amfani da dabarar mawaƙa ta amfani dabarar kwaikwayon mutane har ma da amfani da adon harshe da wasu masana suka kira jinsarwa wasu kuma suka kira shi jinsantarwa. Mawaƙin ya jinsantar da tsuntsaye da karkuna.
Sokoto State University
Title: Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi.
Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” maƙala ce da ta yi nazarin ɗaya daga cikin hikimomin da waƙoƙin Kassu Zurmi suka ƙunsa wato kwaikwayon muryoyi daban-daban na mutane da ma wasu sauran halittu.
Maƙalar ta yi amfani da waƙoƙi kamar waƙar Nomau Namagarya da waƙar Shayi Ɗangidan Labbo da waƙar Muhammadu Fatake na Dare haka kuma ana iya lalubo misalai daga wasu waƙoƙi masu salo makamancin na Kassu Zurmi.
Manufar wannan maƙala ita ce a dubi irin hikimar Kassu wajen kwaikwayo a cikin waƙarsa, sannan a dubi shi kansa kwaikwayon yadda ya rarraba da kuma yadda ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa.
Bincike maƙala dai ta jingina ne falsafar waƙe Magana ta Hausawa da ke cewa « Kai kaɗai gayya” da ma dai Kassu Zurmi ba karɓi ake masa ba, saboda haka duk hira da tattaunawar da ka ji cikin waƙoƙinsa duk shi kaɗai ne ke hidimar sa.
Abin da binciken wannan maƙala ya gano shi Kassu Zurmi ya yi amfani da dabarar mawaƙa ta amfani dabarar kwaikwayon mutane har ma da amfani da adon harshe da wasu masana suka kira jinsarwa wasu kuma suka kira shi jinsantarwa.
Mawaƙin ya jinsantar da tsuntsaye da karkuna.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...

