Javascript must be enabled to continue!
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo mafi ƙayatarwa a waƙoƙin Kassu Zurmi shi ne amfani da ɓoyayyin taurari, wato bayani da yabon mutum ko hali cikin salo na ɓoyewa. Ɓoyayyin taurari a adabi na nufin wasu mutane ko halaye da aka bayyana cikin waƙa ta hanyar nuni ko alama, ba tare da an ambaci sunayen waɗanda suka aikata su kai tsaye ba. Hakan yana buƙatar basira da fahimtar yadda makaɗin ke sarrafa kalmomi cikin tsarin labari amma a sigar waƙa don bayyana su waye ne ɓoyayyin taurari. Wannan nazari da za a gudanar an yi masa suna da ‘Wasu |oyayyin taurari a wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi’. Nazarin zai yi tsinkaye ne a wasu waƙoƙin makaɗin tare da fito da wasu ɗiyan waƙoƙi da makaɗin ya yi amfani da su, wanda a cikin su za a bayyana yadda makaɗin ya ambaci ɓoyayyen tauraro. Nazarin zai taƙaita ne ga waƙoƙi biyu na makaɗin, kuma da su ne za a yi ƙoƙarin fito da ƙudurin wannan maƙala. Waƙoƙin su ne ‘Waƙar Nomau Namagarya’ da ‘Waƙar Na Gidan Duwa Maidabo Gajere Mazaizan Duniya’.
Sokoto State University
Title: Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima.
Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo.
Ɗaya daga cikin salo mafi ƙayatarwa a waƙoƙin Kassu Zurmi shi ne amfani da ɓoyayyin taurari, wato bayani da yabon mutum ko hali cikin salo na ɓoyewa.
Ɓoyayyin taurari a adabi na nufin wasu mutane ko halaye da aka bayyana cikin waƙa ta hanyar nuni ko alama, ba tare da an ambaci sunayen waɗanda suka aikata su kai tsaye ba.
Hakan yana buƙatar basira da fahimtar yadda makaɗin ke sarrafa kalmomi cikin tsarin labari amma a sigar waƙa don bayyana su waye ne ɓoyayyin taurari.
Wannan nazari da za a gudanar an yi masa suna da ‘Wasu |oyayyin taurari a wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi’.
Nazarin zai yi tsinkaye ne a wasu waƙoƙin makaɗin tare da fito da wasu ɗiyan waƙoƙi da makaɗin ya yi amfani da su, wanda a cikin su za a bayyana yadda makaɗin ya ambaci ɓoyayyen tauraro.
Nazarin zai taƙaita ne ga waƙoƙi biyu na makaɗin, kuma da su ne za a yi ƙoƙarin fito da ƙudurin wannan maƙala.
Waƙoƙin su ne ‘Waƙar Nomau Namagarya’ da ‘Waƙar Na Gidan Duwa Maidabo Gajere Mazaizan Duniya’.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

