Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI

View through CrossRef
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ne daga cikin salalan da makada kan yi amfani da shi wajen kwarzanta iyayen gidansu da kambamasu da ƙoƙarin dakushe farin jini da ƙima ta abokan hamayya. Wannan takarda ta bibiyi wasu daga cikin adon harshe a waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi domin fito da irin na sa salon, na yi wa waƙoƙinsa ado da kwalliya da kwarzanta iyayen gidansa da muzanta abokan adawa. An yi amfani da ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) na Gusau (2003). Sannan an yi amfani da nau'in bincike bi sharhi wajen kalailaice bayanan wannan takarda. Takardar ta bibiyi wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi musamman waɗanda ya yi wa 'yan farauta da ‘yantauri da ɓarayi, ta kuma gano yadda Makada Kassu Zurmi ya ke amfani da salon adon harshe domin nuna gwanintar harshe. Haka kuma ta gano ya na kuma amfani da salon adon harshe irin su jinsintarwa da siffantawa da salon kambame da kamantawa na daidaito da fifiko ko kuma na kasawa duk a cikin waƙoƙinsa. Ta kuma gano cewa Makaɗa Kassu ya nakalci harshen Hausa, wannan ya ba shi dama wajen yi wa waƙarsa ado da kwalliya. Adon harshe, Kassu Zurmi,kamantawa, jinsirtarwa, alamtarwa kambam
Title: ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Description:
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza.
Adon harshe salo ne daga cikin salalan da makada kan yi amfani da shi wajen kwarzanta iyayen gidansu da kambamasu da ƙoƙarin dakushe farin jini da ƙima ta abokan hamayya.
Wannan takarda ta bibiyi wasu daga cikin adon harshe a waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi domin fito da irin na sa salon, na yi wa waƙoƙinsa ado da kwalliya da kwarzanta iyayen gidansa da muzanta abokan adawa.
An yi amfani da ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) na Gusau (2003).
Sannan an yi amfani da nau'in bincike bi sharhi wajen kalailaice bayanan wannan takarda.
Takardar ta bibiyi wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi musamman waɗanda ya yi wa 'yan farauta da ‘yantauri da ɓarayi, ta kuma gano yadda Makada Kassu Zurmi ya ke amfani da salon adon harshe domin nuna gwanintar harshe.
Haka kuma ta gano ya na kuma amfani da salon adon harshe irin su jinsintarwa da siffantawa da salon kambame da kamantawa na daidaito da fifiko ko kuma na kasawa duk a cikin waƙoƙinsa.
Ta kuma gano cewa Makaɗa Kassu ya nakalci harshen Hausa, wannan ya ba shi dama wajen yi wa waƙarsa ado da kwalliya.
Adon harshe, Kassu Zurmi,kamantawa, jinsirtarwa, alamtarwa kambam.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
NAZARIN ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
NAZARIN ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Manufar wannan takarda ita ce zaƙulo irin fasahar da hikimar da Allah ya yi wa makaɗa Kassu Zurmi a fagen waƙa, tare da bayyana irin yadda yake amfani da nau’o’in Adon harshe daban...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Back to Top