Javascript must be enabled to continue!
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
View through CrossRef
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi daga ‘ya’ya har jikoki. Wannan ya sa sata ba ta da hurumi ko gindin zama a dukkan sha’anonin Bahaushe, amma sai aka wayi gari ana tsintar waƙoƙi da ake yi wa masu yin sata, watau ɓarayi ke nan. Ta kai har ana yabon dabarunsu (bajintarsu) da yi musu kirari kamar yadda ake yi wa sauran mutane. Da haka aka samu mawaƙa irin su Gambo da Kassu Zurmi da wasu mawaƙa suna yi wa ɓarayi waƙa. Wannan muƙala, ta zaƙulo yadda mawaƙi Kassu Zurmi ya fito da yanaye yanayen sata da nau’o’inta da dabarun yin ta a cikin wasu waƙoƙinsa da ya yi wa ɓarayi duk da yake shi ba makaɗin ɓarayi ba ne, makaɗin tauri da farauta ne, sai dai a ce sha’awa da kwaɗayi suka ja shi ga yin waƙar ɓarayi. Don yana cewa “ba za ni talauci ba, tun da arnan dare na biki, wanda duy yas samu da ni”. Muƙalar kuma ta taɓo kirari da faɗakarwar da Kassu ke yi wa masu kaya a kan ɓarayi da dangantakar ɓarayi da ‘yan tauri da kuma alaƙar Kassu da ɓarayin. Muƙala ta kammala da cewa Kassu ya yi wa ɓarayi farin sani da har yake iya fito da dabarun da suke yi wajen yin sata, da kuma kwaɗayin abin hannunsu da yake yi wanda ya kai shi ga zuwa ci-rani a waƙar ɓarayi. Hasali ma, ya fi samun alheri ga ɓarayi fiye da ga ‘yan tauri, don ko Gambo mai waƙar ɓarayi yana cewa “ A ba ka yau a ba ka gobe, ɓarawo ɗai a hakan ga.” Ra’in da aka ɗora wannan nazarin shi ne, ‘Ra’in Madubin ƙyallaro Al’adu’. Ra’i ne wanda yake nuni da yadda akan yi amfani da adabi ko al’ada ko harshe a matsayin madubi don ƙyallaro al’adun al’umma kamar yadda Ado, (2017: 84) ya bayyana. Hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike sun haɗa da, sauraren waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi a MP da wayar salula da kuma, bitar wasu litattafai da kundaye da muƙalun da aka buga.
Sokoto State University
Title: Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Description:
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi daga ‘ya’ya har jikoki.
Wannan ya sa sata ba ta da hurumi ko gindin zama a dukkan sha’anonin Bahaushe, amma sai aka wayi gari ana tsintar waƙoƙi da ake yi wa masu yin sata, watau ɓarayi ke nan.
Ta kai har ana yabon dabarunsu (bajintarsu) da yi musu kirari kamar yadda ake yi wa sauran mutane.
Da haka aka samu mawaƙa irin su Gambo da Kassu Zurmi da wasu mawaƙa suna yi wa ɓarayi waƙa.
Wannan muƙala, ta zaƙulo yadda mawaƙi Kassu Zurmi ya fito da yanaye yanayen sata da nau’o’inta da dabarun yin ta a cikin wasu waƙoƙinsa da ya yi wa ɓarayi duk da yake shi ba makaɗin ɓarayi ba ne, makaɗin tauri da farauta ne, sai dai a ce sha’awa da kwaɗayi suka ja shi ga yin waƙar ɓarayi.
Don yana cewa “ba za ni talauci ba, tun da arnan dare na biki, wanda duy yas samu da ni”.
Muƙalar kuma ta taɓo kirari da faɗakarwar da Kassu ke yi wa masu kaya a kan ɓarayi da dangantakar ɓarayi da ‘yan tauri da kuma alaƙar Kassu da ɓarayin.
Muƙala ta kammala da cewa Kassu ya yi wa ɓarayi farin sani da har yake iya fito da dabarun da suke yi wajen yin sata, da kuma kwaɗayin abin hannunsu da yake yi wanda ya kai shi ga zuwa ci-rani a waƙar ɓarayi.
Hasali ma, ya fi samun alheri ga ɓarayi fiye da ga ‘yan tauri, don ko Gambo mai waƙar ɓarayi yana cewa “ A ba ka yau a ba ka gobe, ɓarawo ɗai a hakan ga.
” Ra’in da aka ɗora wannan nazarin shi ne, ‘Ra’in Madubin ƙyallaro Al’adu’.
Ra’i ne wanda yake nuni da yadda akan yi amfani da adabi ko al’ada ko harshe a matsayin madubi don ƙyallaro al’adun al’umma kamar yadda Ado, (2017: 84) ya bayyana.
Hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike sun haɗa da, sauraren waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi a MP da wayar salula da kuma, bitar wasu litattafai da kundaye da muƙalun da aka buga.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...

