Javascript must be enabled to continue!
Mata Makusantan ‘Yan Tauri A Bakin Makaɗa Kassu Zurmi
View through CrossRef
Wannan maƙala tana magana a kan matsayi da alaƙar jinsin mata a sana’ar tauri da ‘yan tauri, tare da wasu taurari da suka fito a waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi. Bincike ya fahimci cewa, a al’ummar Hausawa duk irin ɗauki-ba-daɗin da ake na rayuwa ba ya kammala idan ba mata a ciki, domin su ne abokan tafiyar maza.. Waƙoƙin makaɗa Kassu, sun keɓanta kan waƙoƙin maza a ɓangaren tauri da farauta da sata. Waɗannan al'adu ne na jarumtaka da suka ba da }arfi ga jinsin ga maza saboda yanayin halitta da kuma al'adun al’ummar Hausawa, amma wannan bai hana mawaƙin ya ambato wasu ɗaiɗaikun mata abokan tafiya da suke da kusanci da tauri da ‘yan tauri da irin rawar da suka taka a cikin lamarin tauri. Manufar binciken shi ne fito da matsayin waɗannan matan da irin gudummuwarsu ga abokan zamansu. Ma}alar ta yi duba kai-tsaye ga waɗannan matan domin fito da gudummuwarsu a cikin tafiya da kuma irin dangantaka da alaƙar da suke da ita da wasu fitattun ‘yan tauri. Binciken ya tattaro bayanai ta fuska biyu; wato ta bibiyar waƙoƙin mawaƙin domin zaƙulo baitukan da ma waƙoƙin da aka ambacin matan. Akwai yin hira da masana da waɗanda ke da dangantaka da matan don jin wani bayani da ya shafi rayuwarsu da inda suka haɗa da yan tauri. Sakamakon wannan bincike ya yi hasashen cewa mata sun samu matsayi a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, matsayi mai kusanci da sana’ar tauri da ‘yan-tauri daidai jinsinsu da iyawa da ƙwarewarsu a rayuwa.
Sokoto State University
Title: Mata Makusantan ‘Yan Tauri A Bakin Makaɗa Kassu Zurmi
Description:
Wannan maƙala tana magana a kan matsayi da alaƙar jinsin mata a sana’ar tauri da ‘yan tauri, tare da wasu taurari da suka fito a waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi.
Bincike ya fahimci cewa, a al’ummar Hausawa duk irin ɗauki-ba-daɗin da ake na rayuwa ba ya kammala idan ba mata a ciki, domin su ne abokan tafiyar maza.
Waƙoƙin makaɗa Kassu, sun keɓanta kan waƙoƙin maza a ɓangaren tauri da farauta da sata.
Waɗannan al'adu ne na jarumtaka da suka ba da }arfi ga jinsin ga maza saboda yanayin halitta da kuma al'adun al’ummar Hausawa, amma wannan bai hana mawaƙin ya ambato wasu ɗaiɗaikun mata abokan tafiya da suke da kusanci da tauri da ‘yan tauri da irin rawar da suka taka a cikin lamarin tauri.
Manufar binciken shi ne fito da matsayin waɗannan matan da irin gudummuwarsu ga abokan zamansu.
Ma}alar ta yi duba kai-tsaye ga waɗannan matan domin fito da gudummuwarsu a cikin tafiya da kuma irin dangantaka da alaƙar da suke da ita da wasu fitattun ‘yan tauri.
Binciken ya tattaro bayanai ta fuska biyu; wato ta bibiyar waƙoƙin mawaƙin domin zaƙulo baitukan da ma waƙoƙin da aka ambacin matan.
Akwai yin hira da masana da waɗanda ke da dangantaka da matan don jin wani bayani da ya shafi rayuwarsu da inda suka haɗa da yan tauri.
Sakamakon wannan bincike ya yi hasashen cewa mata sun samu matsayi a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, matsayi mai kusanci da sana’ar tauri da ‘yan-tauri daidai jinsinsu da iyawa da ƙwarewarsu a rayuwa.
Related Results
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Wawa Mugunyar Tsirfa, Uba na Fada Uwa Na Kuka: Lalaben Tarihin Karabkiya Tsakanin ‘Yan Tauri a Bakin Makaɗa Kassu Zurmi. Bitar Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa
Wawa Mugunyar Tsirfa, Uba na Fada Uwa Na Kuka: Lalaben Tarihin Karabkiya Tsakanin ‘Yan Tauri a Bakin Makaɗa Kassu Zurmi. Bitar Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa
Kassu fitacce ne a waƙoƙin, noma, farauta, tauri da ɗan’hali. Shi ya sa aka kira shi makaɗin Maza. Ba a kalli Maza a matsayin jinsi ba a nan, sai dai masu ƙarhin hali wajen murza w...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi d...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...

