Javascript must be enabled to continue!
Wawa Mugunyar Tsirfa, Uba na Fada Uwa Na Kuka: Lalaben Tarihin Karabkiya Tsakanin ‘Yan Tauri a Bakin Makaɗa Kassu Zurmi. Bitar Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa
View through CrossRef
Kassu fitacce ne a waƙoƙin, noma, farauta, tauri da ɗan’hali. Shi ya sa aka kira shi makaɗin Maza. Ba a kalli Maza a matsayin jinsi ba a nan, sai dai masu ƙarhin hali wajen murza wasu ayyuka masu wuya ta fuskar gwarzontaka. Wanda ko ya koma daji ya tare a muhalli ɗaya da miyagun ƙwari da namun daji waɗanda Allah ya keɓe su a dajin, da wanda ya wulaƙanta darensa da ranarsa domin ya firgita wanda ya samu halaliyarsa a tsakiyar daren da rana ya kwace masa ƙotonsa, wato mai ɗan hali, in aka haɗa da wanda kullum tunaninsa bai fi nuna buwaya ba a bayyane da ɓoye ba, wato Dantauri, to waɗannan su ne Kassu ya shahara wajen yi ma waƙa. Na daɗe ina tattara waƙoƙin Kassu. Na mayyeze ƙumshiyarsu kamar yadda nissan Kassun shi kansa. Na sha binsa ina neman tafsirin fasaharsa tun ina Dankachaurana. Na ga lokaci ya yi da zan ɓarge gumina domin tabbatar ma ɗalibai ‘yan uwana cewa Kassu fasihi ne ta fuskar adana tarihin waɗanda suka yi sunan su maza ne musamman a cikin al’ummarsa. Wannan tsakure zai taƙaita kansa ne a nazarin wata karabkiyar da ta wanzu tsawon zamunna tsakanin ‘yan Tauri na yankin da shi mawaƙin ya yi nasa zamani. Sai mun haɗu a cikin zubin wannan maƙala domin ku sha labari.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Wawa Mugunyar Tsirfa, Uba na Fada Uwa na Kuka: Lalaben Tarihin Karabkiya Tsakanin ‘Yan Tauri a Bakin Makaɗa Kassu Zurmi. Bitar Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa
Sokoto State University
Title: Wawa Mugunyar Tsirfa, Uba na Fada Uwa Na Kuka: Lalaben Tarihin Karabkiya Tsakanin ‘Yan Tauri a Bakin Makaɗa Kassu Zurmi. Bitar Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa
Description:
Kassu fitacce ne a waƙoƙin, noma, farauta, tauri da ɗan’hali.
Shi ya sa aka kira shi makaɗin Maza.
Ba a kalli Maza a matsayin jinsi ba a nan, sai dai masu ƙarhin hali wajen murza wasu ayyuka masu wuya ta fuskar gwarzontaka.
Wanda ko ya koma daji ya tare a muhalli ɗaya da miyagun ƙwari da namun daji waɗanda Allah ya keɓe su a dajin, da wanda ya wulaƙanta darensa da ranarsa domin ya firgita wanda ya samu halaliyarsa a tsakiyar daren da rana ya kwace masa ƙotonsa, wato mai ɗan hali, in aka haɗa da wanda kullum tunaninsa bai fi nuna buwaya ba a bayyane da ɓoye ba, wato Dantauri, to waɗannan su ne Kassu ya shahara wajen yi ma waƙa.
Na daɗe ina tattara waƙoƙin Kassu.
Na mayyeze ƙumshiyarsu kamar yadda nissan Kassun shi kansa.
Na sha binsa ina neman tafsirin fasaharsa tun ina Dankachaurana.
Na ga lokaci ya yi da zan ɓarge gumina domin tabbatar ma ɗalibai ‘yan uwana cewa Kassu fasihi ne ta fuskar adana tarihin waɗanda suka yi sunan su maza ne musamman a cikin al’ummarsa.
Wannan tsakure zai taƙaita kansa ne a nazarin wata karabkiyar da ta wanzu tsawon zamunna tsakanin ‘yan Tauri na yankin da shi mawaƙin ya yi nasa zamani.
Sai mun haɗu a cikin zubin wannan maƙala domin ku sha labari.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Wawa Mugunyar Tsirfa, Uba na Fada Uwa na Kuka: Lalaben Tarihin Karabkiya Tsakanin ‘Yan Tauri a Bakin Makaɗa Kassu Zurmi.
Bitar Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi...
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...

