Javascript must be enabled to continue!
Gurbin Musulunci A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Mawaƙan Hausa mutane ne da Allah ya yi wa baiwa da basira da hikimomi wajen tsara zantuttukan hikima a cikin baitocin waƙa ko ɗiyan waƙa. Wannan baiwa da Allah ya yi musu ya sa ake tsintar abubuwa nagartattu da yawa waɗanda suka shafi hanyoyin rayuwar al’umma a cikin waƙoƙinsu. Da ma shi harshe sha-kundum ne a rayuwar kowace al’umma domin shi ke bayyana kowane irin al’amari da zai fito cikin al’umma musamman fasahohinsu na baka. A dalilin haka ne aka shirya wannan maƙala da aka yi wa take da Gurbin Musulunci a wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi. Wannan maƙala ta ƙudiri fito da wasu abubuwa da Kassu Zurmi ya ambata a cikin ɗiyan wasu waƙoƙinsa da ya yi, waɗanda nazari ya gano cewa ko shakka babu abubuwan an ambace su ne a dalilin tasirin da addinin Musulunci ya yi a rayuwar mawaƙin. An zaɓi waƙoƙi biyu daga cikin waƙoƙin da mawaƙin ya yi domin fito da ƙudirin maƙalar. Waƙoƙin su ne ‘Waƙar Iro Shayi ɗan gidan Labbo’ da ‘Waƙar Malam Sanda ɗan Ruhwa’i’.
Sokoto State University
Title: Gurbin Musulunci A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Mawaƙan Hausa mutane ne da Allah ya yi wa baiwa da basira da hikimomi wajen tsara zantuttukan hikima a cikin baitocin waƙa ko ɗiyan waƙa.
Wannan baiwa da Allah ya yi musu ya sa ake tsintar abubuwa nagartattu da yawa waɗanda suka shafi hanyoyin rayuwar al’umma a cikin waƙoƙinsu.
Da ma shi harshe sha-kundum ne a rayuwar kowace al’umma domin shi ke bayyana kowane irin al’amari da zai fito cikin al’umma musamman fasahohinsu na baka.
A dalilin haka ne aka shirya wannan maƙala da aka yi wa take da Gurbin Musulunci a wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi.
Wannan maƙala ta ƙudiri fito da wasu abubuwa da Kassu Zurmi ya ambata a cikin ɗiyan wasu waƙoƙinsa da ya yi, waɗanda nazari ya gano cewa ko shakka babu abubuwan an ambace su ne a dalilin tasirin da addinin Musulunci ya yi a rayuwar mawaƙin.
An zaɓi waƙoƙi biyu daga cikin waƙoƙin da mawaƙin ya yi domin fito da ƙudirin maƙalar.
Waƙoƙin su ne ‘Waƙar Iro Shayi ɗan gidan Labbo’ da ‘Waƙar Malam Sanda ɗan Ruhwa’i’.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...