Javascript must be enabled to continue!
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
View through CrossRef
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya dubi hoton faɗi-tashin auren Bahaushe a waƙar Makaɗa Abubakar Kasssu Zurmi wadda ya rera wa tauraronsa mai suna Shayi Ɗangidan Labbo. Nazarin ya yi ƙoƙarin dubin wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar masu alaƙa da shi a matakan ilimi daban-daban. An yi hakan ne saboda a gano giɓin da magabata suka bari, saboda a san yadda za a cike shi. An yi ƙoƙarin yin amfani da hanyoyin tattara bayanai waɗanda suka haɗa da, sauraron waƙar Shayi Ɗangidan Labbo daga bakin wanda ya rera ta a cikin na’urar adana bayanai ta memori. Haka kuma, an yi ƙoƙarin karanta waƙar a cikin rubuce-rubucen wasu masana da suka taskance ta. Baya ga haka, binciken bai yi ƙasa a guiwa ba wajen tuntuɓar masana al’adun aure na Hausawa da kuma waɗanda suka fahimci waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi. An yi wa aikin farfajiya da waƙar Shayi Ɗangidan Labbo kaɗai, domin kada a wuce makaɗi da rawa. Wasu daga cikin sakamakon da nazarin ya bayyana sun haɗa da: Binciken ya gano yadda Makaɗi Kassu Zurmi ya fitar da wasu ɗabi’u da halaye mara kyau ga masu neman aure waɗanda idan ba a kula da su ba a wajen zaɓin miji za su zama ƙalubale ga rayuwar ma’aurata. Wannan ya tabbatar da gudummuwar da makaɗin ya bayar wajen bunƙasa al’adun Hausawa. Haka kuma, nazarin ya gano cewa, makaɗa ya yi wa iyaye hannunka-mai-sanda musamman a wajen bayar da ɗiyarsu aure don gudun kada a faɗa hannun bara-gurbi.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Faɗi-tashi, Aure da kuma Bahaushe
Sokoto State University
Title: Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Description:
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa.
Buƙatar wannan nazari ne ya dubi hoton faɗi-tashin auren Bahaushe a waƙar Makaɗa Abubakar Kasssu Zurmi wadda ya rera wa tauraronsa mai suna Shayi Ɗangidan Labbo.
Nazarin ya yi ƙoƙarin dubin wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar masu alaƙa da shi a matakan ilimi daban-daban.
An yi hakan ne saboda a gano giɓin da magabata suka bari, saboda a san yadda za a cike shi.
An yi ƙoƙarin yin amfani da hanyoyin tattara bayanai waɗanda suka haɗa da, sauraron waƙar Shayi Ɗangidan Labbo daga bakin wanda ya rera ta a cikin na’urar adana bayanai ta memori.
Haka kuma, an yi ƙoƙarin karanta waƙar a cikin rubuce-rubucen wasu masana da suka taskance ta.
Baya ga haka, binciken bai yi ƙasa a guiwa ba wajen tuntuɓar masana al’adun aure na Hausawa da kuma waɗanda suka fahimci waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi.
An yi wa aikin farfajiya da waƙar Shayi Ɗangidan Labbo kaɗai, domin kada a wuce makaɗi da rawa.
Wasu daga cikin sakamakon da nazarin ya bayyana sun haɗa da: Binciken ya gano yadda Makaɗi Kassu Zurmi ya fitar da wasu ɗabi’u da halaye mara kyau ga masu neman aure waɗanda idan ba a kula da su ba a wajen zaɓin miji za su zama ƙalubale ga rayuwar ma’aurata.
Wannan ya tabbatar da gudummuwar da makaɗin ya bayar wajen bunƙasa al’adun Hausawa.
Haka kuma, nazarin ya gano cewa, makaɗa ya yi wa iyaye hannunka-mai-sanda musamman a wajen bayar da ɗiyarsu aure don gudun kada a faɗa hannun bara-gurbi.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Faɗi-tashi, Aure da kuma Bahaushe.
Related Results
Nazarin Neman Auren Hausawa a Cikin Waƙar Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi Ta Shayi Ɗan Gidan Labbo
Nazarin Neman Auren Hausawa a Cikin Waƙar Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi Ta Shayi Ɗan Gidan Labbo
Wannan maƙala ta yi nazarin neman auren Hausawa a cikin waƙar Makaɗa Abubakar Kassu Zurni ta Shayi ɗan gidan Labbo. Manufar wannan maƙala ita ce, fito da wasu al’adun neman aure, ...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi d...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Kwatancin Halayen Masu Nakasar Kisan-Raɓa Tsakanin Al’umma Da ‘Yan Taurin Kassu Zurmi
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ...

