Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Nau’o’in Abincin Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi

View through CrossRef
Wannan maƙala ta bibiyi wasu waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi, domin fito da nau’o’in abincin Hausawa na gargajiya da suke ƙunshe a ciki. Haka kuma, maƙalar ta kafa hujja da waɗansu ɗiyan waƙoƙi da suke tabbatar da cewa, zane na mai shi ne, kowa ya laga aro ya yi. Watau kenan, duk nau’o’in abincin da Kassu Zurmi ya ambata a cikin ɗiyan waƙoƙin da aka kawo a cikin wannan maƙala, to abincin Hausawa ne. Sai dai dalilin cuɗanya da waɗansu baƙi al’umma, ya sa a yanzu an samu ƙarin nau’ukan abinci da Hausawa suke amfani da shi wanɗanda ba na gargajiya ba ne. Daga cikin abubuwan da wannan maƙala ta gano su ne, dalilin cuɗanya da baƙin al’umma, Hausawa wasu sun fara raja’a ga sababbin nau’ukan abincin zamani saɓanin na gargajiya. Ƙananan yara masu tasowa kuma, ba su san sunayen nau’ukan abincin Hausawa na gargajiya ba.
Title: Nau’o’in Abincin Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Wannan maƙala ta bibiyi wasu waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi, domin fito da nau’o’in abincin Hausawa na gargajiya da suke ƙunshe a ciki.
Haka kuma, maƙalar ta kafa hujja da waɗansu ɗiyan waƙoƙi da suke tabbatar da cewa, zane na mai shi ne, kowa ya laga aro ya yi.
Watau kenan, duk nau’o’in abincin da Kassu Zurmi ya ambata a cikin ɗiyan waƙoƙin da aka kawo a cikin wannan maƙala, to abincin Hausawa ne.
Sai dai dalilin cuɗanya da waɗansu baƙi al’umma, ya sa a yanzu an samu ƙarin nau’ukan abinci da Hausawa suke amfani da shi wanɗanda ba na gargajiya ba ne.
Daga cikin abubuwan da wannan maƙala ta gano su ne, dalilin cuɗanya da baƙin al’umma, Hausawa wasu sun fara raja’a ga sababbin nau’ukan abincin zamani saɓanin na gargajiya.
Ƙananan yara masu tasowa kuma, ba su san sunayen nau’ukan abincin Hausawa na gargajiya ba.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...

Back to Top