Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi

View through CrossRef
Duk wani abu da ya shafi fasahar bayyana nagartaccen tsarin rayuwa ta mutum da kuma al’umma wadda ta shafi duniya da wadda ta shafi Lahira tana nan tule a cikin waƙoƙin baka na Hausa (Gusau, 2014). Alhaji Kassu Zurmi yana ɗaya daga cikin mawaƙan baka na Hausa, wanda Allah ya ba shi basira da hazaƙa da fasaha da hikimar naƙaltar harshen Hausa da adabi da abin da ya shafi al’adun Hausawa tun daga sana’a da muhalli da aure, da haihuwa da kuma sunayen Hausawa na kafin musulunci da kuma bayan musulunci. Don haka, Kassu Zurmi mawaƙi ne na maza, wato mafarauta da ‘yan tauri da ɓarayi, saboda haka, waƙoƙinsa ƙunshe suke da sunayen Hausawa na gargajiya tun kafin musulunci da kuma waɗanda suka samu bayan zuwan musulunci. Akwai ayyuka da dama daga masana da masu bincike a dangane da abin da ya shafi ma’anar suna da sunayen Hausawa na gargajiya da kwatanta sunayen gargajiya na Hausawa da kuma kiran sunan mutum na asali tare da laƙabin garinsu ko unguwarsu da abin da ya shafi sakaya suna na asali na Bahaushe.
Title: Sunayen Hausawa na Gargajiya a Cikin Waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi
Description:
Duk wani abu da ya shafi fasahar bayyana nagartaccen tsarin rayuwa ta mutum da kuma al’umma wadda ta shafi duniya da wadda ta shafi Lahira tana nan tule a cikin waƙoƙin baka na Hausa (Gusau, 2014).
Alhaji Kassu Zurmi yana ɗaya daga cikin mawaƙan baka na Hausa, wanda Allah ya ba shi basira da hazaƙa da fasaha da hikimar naƙaltar harshen Hausa da adabi da abin da ya shafi al’adun Hausawa tun daga sana’a da muhalli da aure, da haihuwa da kuma sunayen Hausawa na kafin musulunci da kuma bayan musulunci.
Don haka, Kassu Zurmi mawaƙi ne na maza, wato mafarauta da ‘yan tauri da ɓarayi, saboda haka, waƙoƙinsa ƙunshe suke da sunayen Hausawa na gargajiya tun kafin musulunci da kuma waɗanda suka samu bayan zuwan musulunci.
Akwai ayyuka da dama daga masana da masu bincike a dangane da abin da ya shafi ma’anar suna da sunayen Hausawa na gargajiya da kwatanta sunayen gargajiya na Hausawa da kuma kiran sunan mutum na asali tare da laƙabin garinsu ko unguwarsu da abin da ya shafi sakaya suna na asali na Bahaushe.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...

Back to Top