Javascript must be enabled to continue!
Gurbin Sana’o’in Gargajiyar Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Babbar manufar maƙalar ita ce fito da sana’o’in gargajiya na Hausawa, waɗanda Kassu Zurmi ya taskace a cikin waƙoƙinsa tare da duban yadda shi makaɗin ya kalle su a cikin waƙoƙinsa, kuma a fito da gudummuwar da suke bayarwa wajen inganta tare da bunƙasa tattalin arziƙin Hausawa. An yi ƙoƙarin fito da dangantakar da sana’o’in da aka ambata a cikin waƙoƙin suke da shi da kuma yadda hakan yake samar da kyakkyawan yanayi na cuɗanni-in-cuɗe-ka a tsakanin sana’o’in na gargajiya. An yi amfani da hanyoyi da dama wajen tattara bayanan da aka yi amfani da su wajen gina wannan maƙala. Hanyoyin sun haɗa da, yin hira da masana, musamman na waƙoƙin baka da nazarce-nazarcen littattafai da kundayen da magabata suka rubuta a kan waƙoƙin Kassu Zurmi. Har wa yau, an saurari waƙoƙinsa da aka naɗa a faya-fayen sidi na rediyo da na talabijin. Binciken ya gano yadda Hausawa suka ɗauki sana’o’insu na gargajiya da daraja, kuma abin dogarau wajen neman na kai da kare mutunci. Haka kuma, Hausawa na matuƙar alfahari da sana’o’insu na gado, kuma suna kare martabarsu a duk inda suka samu kan su ba tare da jin tsoro ko fargaba ba.
Sokoto State University
Title: Gurbin Sana’o’in Gargajiyar Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Babbar manufar maƙalar ita ce fito da sana’o’in gargajiya na Hausawa, waɗanda Kassu Zurmi ya taskace a cikin waƙoƙinsa tare da duban yadda shi makaɗin ya kalle su a cikin waƙoƙinsa, kuma a fito da gudummuwar da suke bayarwa wajen inganta tare da bunƙasa tattalin arziƙin Hausawa.
An yi ƙoƙarin fito da dangantakar da sana’o’in da aka ambata a cikin waƙoƙin suke da shi da kuma yadda hakan yake samar da kyakkyawan yanayi na cuɗanni-in-cuɗe-ka a tsakanin sana’o’in na gargajiya.
An yi amfani da hanyoyi da dama wajen tattara bayanan da aka yi amfani da su wajen gina wannan maƙala.
Hanyoyin sun haɗa da, yin hira da masana, musamman na waƙoƙin baka da nazarce-nazarcen littattafai da kundayen da magabata suka rubuta a kan waƙoƙin Kassu Zurmi.
Har wa yau, an saurari waƙoƙinsa da aka naɗa a faya-fayen sidi na rediyo da na talabijin.
Binciken ya gano yadda Hausawa suka ɗauki sana’o’insu na gargajiya da daraja, kuma abin dogarau wajen neman na kai da kare mutunci.
Haka kuma, Hausawa na matuƙar alfahari da sana’o’insu na gado, kuma suna kare martabarsu a duk inda suka samu kan su ba tare da jin tsoro ko fargaba ba.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...