Javascript must be enabled to continue!
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Al’adun kyautata zamantakewa, al’adu ne masu ɗimbin yawa da har yau ba a ƙayyade su ba, da ma dai al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Don haka dukkan tsarin da al’adar mutane ta yarda da shi, bin sa kyautatawa ne kuma kauce masa na hardasa rashin kyautatawa. Makaɗa Kassu Zurmi fitaccen makaɗin maza ne, duk da cewa a baya ya yi wa ɓarayi waƙa. Wannan maƙalar tana da manufar fito da wasu al’adun Hausawa na kyautata zamantakewa a cikin wasu waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi. Haka kuma za a nazarci al’adun tare da fayyace muhimmancin riƙo da su. Za a yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu domin cimma burin wannan maƙala. Hanyar ɗora aiki da aka yi amfani da ita kuwa, ita ce ta amfani da karin maganar nan ta “Da tsohuwar zuma ake magani”. Sakamakon wannan maƙala ya gano cewa akwai nason wasu al’adun kyautata zamantakewa a cikin waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi duk kuwa da cewa wasu waƙoƙin ya yi su ne ga masu iƙirarin tsiya kamar yadda ya kira wasu daga cikinsu (‘yan tauri).
Sokoto State University
Title: Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Al’adun kyautata zamantakewa, al’adu ne masu ɗimbin yawa da har yau ba a ƙayyade su ba, da ma dai al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa.
Don haka dukkan tsarin da al’adar mutane ta yarda da shi, bin sa kyautatawa ne kuma kauce masa na hardasa rashin kyautatawa.
Makaɗa Kassu Zurmi fitaccen makaɗin maza ne, duk da cewa a baya ya yi wa ɓarayi waƙa.
Wannan maƙalar tana da manufar fito da wasu al’adun Hausawa na kyautata zamantakewa a cikin wasu waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi.
Haka kuma za a nazarci al’adun tare da fayyace muhimmancin riƙo da su.
Za a yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu domin cimma burin wannan maƙala.
Hanyar ɗora aiki da aka yi amfani da ita kuwa, ita ce ta amfani da karin maganar nan ta “Da tsohuwar zuma ake magani”.
Sakamakon wannan maƙala ya gano cewa akwai nason wasu al’adun kyautata zamantakewa a cikin waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi duk kuwa da cewa wasu waƙoƙin ya yi su ne ga masu iƙirarin tsiya kamar yadda ya kira wasu daga cikinsu (‘yan tauri).
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...