Javascript must be enabled to continue!
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
View through CrossRef
Wannan takarda ta yi nazarin salon da mawaƙi Kassu Zurmi yake amfani da shi ne a waƙarasa wajen bayar da labarin baka a cikin waƙoƙin da yake yi. Manufar takardar ne ta nazarci irin wannan salon na bayar da labari a waƙar da aka yi ta Sarkin Gabas na Gusau. A cikin waƙar Kassu ya faɗi yadda ta kaya a tafiyarsu Daba Gusau, musammam abin da ya faru a garin Bunguɗu. An yi ƙoƙarin fito da irin hikimar da Kassu yake bi wajen jawo hankalin masu sauraron waƙarsa ta hanyar bayar da labarin baka. An ɗora wannan aikin bisa ra’in Nazarin Salon Bayar da Labari a Waƙar Baka ta makarantar Gusau (1999). Nazarin ya fito da salon bayar da labarin baka cikin rauji da kiɗi. Gusau (2008) yana mai cewa mawaƙa da makaɗan baka kan aiwatar da waƙoƙi kan wasu abubuwa da suka faru a tarihi wanda ba koyaushe ake samun hakan ba a wasu waƙoƙin. Wannan nazari ya dace da samun salon bayar da tarihin abin da ya faru na gumurzun maza kamar yadda aka kawo a cikin waƙar ta Sarkin Gabas a tafiyarsu Daba da irin abin da ay biyu bayan hakan a Bunguɗu. Muhimman Kalmomi: baka, hikima, labari, salo, da waƙa
Sokoto State University
Title: Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Description:
Wannan takarda ta yi nazarin salon da mawaƙi Kassu Zurmi yake amfani da shi ne a waƙarasa wajen bayar da labarin baka a cikin waƙoƙin da yake yi.
Manufar takardar ne ta nazarci irin wannan salon na bayar da labari a waƙar da aka yi ta Sarkin Gabas na Gusau.
A cikin waƙar Kassu ya faɗi yadda ta kaya a tafiyarsu Daba Gusau, musammam abin da ya faru a garin Bunguɗu.
An yi ƙoƙarin fito da irin hikimar da Kassu yake bi wajen jawo hankalin masu sauraron waƙarsa ta hanyar bayar da labarin baka.
An ɗora wannan aikin bisa ra’in Nazarin Salon Bayar da Labari a Waƙar Baka ta makarantar Gusau (1999).
Nazarin ya fito da salon bayar da labarin baka cikin rauji da kiɗi.
Gusau (2008) yana mai cewa mawaƙa da makaɗan baka kan aiwatar da waƙoƙi kan wasu abubuwa da suka faru a tarihi wanda ba koyaushe ake samun hakan ba a wasu waƙoƙin.
Wannan nazari ya dace da samun salon bayar da tarihin abin da ya faru na gumurzun maza kamar yadda aka kawo a cikin waƙar ta Sarkin Gabas a tafiyarsu Daba da irin abin da ay biyu bayan hakan a Bunguɗu.
Muhimman Kalmomi: baka, hikima, labari, salo, da waƙa.
Related Results
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Makaɗa suna amfani da wani nao’in salo da ake kira salon dibilwa, a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani salo ne na nuna gwanintar harshe da ƙwarewa ta yadda sukan kawo wata kalma da a...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...

