Javascript must be enabled to continue!
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
View through CrossRef
Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni cikin salo mabambanta, wato ta baka ko rubutacciya.Waƙoƙin baka da rubutattu hanya ce mai gamsarwa wajen isar da saƙo. A wannan maƙala, an yi ƙoƙarin bibiyar waƙar Sa’idu Faru ne makaɗan baka, kuma makaɗan fada, domin fito da irin hikima da fikira da zalaƙa da basirar da Allah ya ba shi wajen sarrafa harshe. A cikin wannan waƙa, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kwalliya da nuna darajar da Sarki yake ɗauka da shi, inda yake siffanta Sarkin Zazzau da wasu dabbobi masu daraja da ƙrfi da kwarjini. Haka kuma da danganta shi da gidan da ya fito na sarauta. Nazarin zai taɓo waƙar da Sa’idy Faru ya yi wa Sarkin da taƙaitaccen tarihin Sarkin da ire-iren kirarin da ake masa a wurare mabambanta. An bi hanyoyi da ya kamata da amfani da dabaru akan yi ƙoƙarin nemo waƙar ta Sarkin Zazzau da sauraronta; don zaƙulo bayanan da ake buƙata a waƙar, da kuma saƙon zuwa ga gaɓar da ake magana a kai. An yi ƙoƙarin ɗora wannan bincike a kan Ra’in mazahabar Nason Adabi a Al’adu (Folk – Cultural Theory) wanda William Bascom ya ƙirƙira, sannan kuma aka samu mabiya daga ƙasar Amurka waɗanda suka bunƙasa shi. Binciken ya ƙare da sakamakon da aka samu yayin gudanarwa.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Description:
Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni cikin salo mabambanta, wato ta baka ko rubutacciya.
Waƙoƙin baka da rubutattu hanya ce mai gamsarwa wajen isar da saƙo.
A wannan maƙala, an yi ƙoƙarin bibiyar waƙar Sa’idu Faru ne makaɗan baka, kuma makaɗan fada, domin fito da irin hikima da fikira da zalaƙa da basirar da Allah ya ba shi wajen sarrafa harshe.
A cikin wannan waƙa, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kwalliya da nuna darajar da Sarki yake ɗauka da shi, inda yake siffanta Sarkin Zazzau da wasu dabbobi masu daraja da ƙrfi da kwarjini.
Haka kuma da danganta shi da gidan da ya fito na sarauta.
Nazarin zai taɓo waƙar da Sa’idy Faru ya yi wa Sarkin da taƙaitaccen tarihin Sarkin da ire-iren kirarin da ake masa a wurare mabambanta.
An bi hanyoyi da ya kamata da amfani da dabaru akan yi ƙoƙarin nemo waƙar ta Sarkin Zazzau da sauraronta; don zaƙulo bayanan da ake buƙata a waƙar, da kuma saƙon zuwa ga gaɓar da ake magana a kai.
An yi ƙoƙarin ɗora wannan bincike a kan Ra’in mazahabar Nason Adabi a Al’adu (Folk – Cultural Theory) wanda William Bascom ya ƙirƙira, sannan kuma aka samu mabiya daga ƙasar Amurka waɗanda suka bunƙasa shi.
Binciken ya ƙare da sakamakon da aka samu yayin gudanarwa.
Related Results
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Wannan maƙala ta karkata ne a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, musamman waɗanda ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Aikin an yi shi ne a kan al’ada domin ya fito da...
Takalmin Kaza Mutuwa Ka Raba: Waiwayen Dangantakar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III Da Makaɗa Sa’idu Faru
Takalmin Kaza Mutuwa Ka Raba: Waiwayen Dangantakar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III Da Makaɗa Sa’idu Faru
Maƙala kan Marigayi Makaɗa Sa’idu Faru ta ginu domin shiga sahun marubuta maƙalu domin samar da kundin da ke ƙunshe da nazarin waƙoƙin Sa’idu Farun don karrama Mai’alfarma Sarkin M...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa. Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru...
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Wannan takarda ta yi nazarin salon da mawaƙi Kassu Zurmi yake amfani da shi ne a waƙarasa wajen bayar da labarin baka a cikin waƙoƙin da yake yi. Manufar takardar ne ta nazarci iri...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Patients with History of Intravenous Drug Use (IDU) with Septic Arthritis of the Foot and Ankle Have Suboptimal Hospitalization Outcomes Compared to Patients Without IDU
Patients with History of Intravenous Drug Use (IDU) with Septic Arthritis of the Foot and Ankle Have Suboptimal Hospitalization Outcomes Compared to Patients Without IDU
Category:
Infection
Introduction/Purpose:
Although intravenous drug use (IDU) is a...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...

