Javascript must be enabled to continue!
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
View through CrossRef
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa. Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru yana daga cikinsu. Wannan muƙala ta gudana ne a kan nazarin Sakkwatanci a waƙar Makaɗa Sa’idu Faru. Manufar muƙala ita ce, zurfafa nazari da fitowa da kalmomin Sakkwatanci a cikin waƙar makaɗa Sa’idu Faru tare da kawo Daidaitacciyar Hausa da kuma nuna bambancin da ke tsakaninsu. Muƙalar ta yi ƙoƙarin tattara bayanai ta hanyar amfani da dabarar sauraren waƙar makaɗa ta: ‘Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo’. A yayin sauraron waƙar, an fito da kalmomin da suka shafi Sakkwatanci tare da kwatanta su da Daidaitacciyar Hausa. An yi amfani da ra’in ‘Tsarin Karin Harshe’ (Generative Dialectology) wanda yake nuna cewa, ana iya nazarin kare-karen harshe daban-daban tare da lura da inda suka yi tarayya da kuma kwatanta shi da Daidaitacciyar Hausa domin fito da bambance-bambancen da ake iya samu tsakaninsu. Ra’in yana da dangantaka da wannan bincike, domin ya yi magana a kan kare-karen harshe da siffofinsa na bai ɗaya. Sakamakon bincike ya tabbatar da cewa, mawaƙa suna amfani da karin harshe a yayin rera waƙoƙinsu, musamman karin harshe na garuruwa da suka fito. Hakazalika, muƙala ta fito da bambancin da ake samu tsakanin karin harshen Sakkwatanci da Daidaitacciyar Hausa.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Description:
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa.
Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru yana daga cikinsu.
Wannan muƙala ta gudana ne a kan nazarin Sakkwatanci a waƙar Makaɗa Sa’idu Faru.
Manufar muƙala ita ce, zurfafa nazari da fitowa da kalmomin Sakkwatanci a cikin waƙar makaɗa Sa’idu Faru tare da kawo Daidaitacciyar Hausa da kuma nuna bambancin da ke tsakaninsu.
Muƙalar ta yi ƙoƙarin tattara bayanai ta hanyar amfani da dabarar sauraren waƙar makaɗa ta: ‘Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo’.
A yayin sauraron waƙar, an fito da kalmomin da suka shafi Sakkwatanci tare da kwatanta su da Daidaitacciyar Hausa.
An yi amfani da ra’in ‘Tsarin Karin Harshe’ (Generative Dialectology) wanda yake nuna cewa, ana iya nazarin kare-karen harshe daban-daban tare da lura da inda suka yi tarayya da kuma kwatanta shi da Daidaitacciyar Hausa domin fito da bambance-bambancen da ake iya samu tsakaninsu.
Ra’in yana da dangantaka da wannan bincike, domin ya yi magana a kan kare-karen harshe da siffofinsa na bai ɗaya.
Sakamakon bincike ya tabbatar da cewa, mawaƙa suna amfani da karin harshe a yayin rera waƙoƙinsu, musamman karin harshe na garuruwa da suka fito.
Hakazalika, muƙala ta fito da bambancin da ake samu tsakanin karin harshen Sakkwatanci da Daidaitacciyar Hausa.
Related Results
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
A taxonomic monograph of the genus Dodomeira Bellò & Baviera, a new genus of Peritelini from Sicily (Coleoptera: Curculionidae: Entiminae)
A taxonomic monograph of the genus Dodomeira Bellò & Baviera, a new genus of Peritelini from Sicily (Coleoptera: Curculionidae: Entiminae)
The genus Dodomeira Bellò & Baviera gen. n. of the tribe Peritelini Lacordaire (1863) (Curculionidae: Entiminae) which includes 39 species is described. Seven species are trans...
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Wannan maƙala ta karkata ne a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, musamman waɗanda ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Aikin an yi shi ne a kan al’ada domin ya fito da...
Takalmin Kaza Mutuwa Ka Raba: Waiwayen Dangantakar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III Da Makaɗa Sa’idu Faru
Takalmin Kaza Mutuwa Ka Raba: Waiwayen Dangantakar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III Da Makaɗa Sa’idu Faru
Maƙala kan Marigayi Makaɗa Sa’idu Faru ta ginu domin shiga sahun marubuta maƙalu domin samar da kundin da ke ƙunshe da nazarin waƙoƙin Sa’idu Farun don karrama Mai’alfarma Sarkin M...
Sassan Waƙa ‘‘Ta Tsaru!’’ a ‘Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa’
Sassan Waƙa ‘‘Ta Tsaru!’’ a ‘Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa’
Tsakure: A gargajiyance, ta alƙalamin Sadaukin Shaihin Malami Abdulƙadir Ɗangambo, Hausawa kan hukumta waƙa da ɗayan matakai huɗu na yabo ko kushewa (Ɗangambo, 2007: 7-9). Wannan m...
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni cikin salo mabambanta, wato ta baka ko rubutacciya.Waƙoƙin baka da rubutattu hanya ce mai gamsarwa wajen isar da saƙo. A wannan maƙala, an y...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...

