Javascript must be enabled to continue!
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
View through CrossRef
Wannan maƙala ta karkata ne a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, musamman waɗanda ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Aikin an yi shi ne a kan al’ada domin ya fito da ɓirɓishin kore da Sa’idu Faru ya yi amfani da shi wajen bayyana wa al’umma matsayi da daraja da nagartar da Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo yake da wadda ta fifita shi a cikin sauran jikokin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Da nuna ya fi kowa cancantar ya gadi mahaifinsa Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar na uku, idan mai rabawa ta raba. An ɗora aikin a bisa karin maganar Hausawa da ke cewa: “Ko kana da kyau ka ƙara da wanka”. Ganin yadda Makaɗa Sa’idu Faru ya yaba ɗabi’u da halaye na Sarkin Kudun Sakkwato duk da ya san jama’a suna da masaniya game da abubuwan da ya ambata a kan Alhaji Muhammadu Macciɗo na nasaba da kyawawan ɗabi’u. Sakamakon binciken ya gano cewa saƙon Sa’idu Faru ya isa a wurin da ya dace ya isa, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Sarkin Kudun Sakkwato ya gadi mahaifinsa a matsayin Sarkin Musulmi. Sai dai Allah bai kai rayuwar Sa’idu Faru wannan lokaci ba.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Description:
Wannan maƙala ta karkata ne a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, musamman waɗanda ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo.
Aikin an yi shi ne a kan al’ada domin ya fito da ɓirɓishin kore da Sa’idu Faru ya yi amfani da shi wajen bayyana wa al’umma matsayi da daraja da nagartar da Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo yake da wadda ta fifita shi a cikin sauran jikokin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.
Da nuna ya fi kowa cancantar ya gadi mahaifinsa Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar na uku, idan mai rabawa ta raba.
An ɗora aikin a bisa karin maganar Hausawa da ke cewa: “Ko kana da kyau ka ƙara da wanka”.
Ganin yadda Makaɗa Sa’idu Faru ya yaba ɗabi’u da halaye na Sarkin Kudun Sakkwato duk da ya san jama’a suna da masaniya game da abubuwan da ya ambata a kan Alhaji Muhammadu Macciɗo na nasaba da kyawawan ɗabi’u.
Sakamakon binciken ya gano cewa saƙon Sa’idu Faru ya isa a wurin da ya dace ya isa, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Sarkin Kudun Sakkwato ya gadi mahaifinsa a matsayin Sarkin Musulmi.
Sai dai Allah bai kai rayuwar Sa’idu Faru wannan lokaci ba.
Related Results
Takalmin Kaza Mutuwa Ka Raba: Waiwayen Dangantakar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III Da Makaɗa Sa’idu Faru
Takalmin Kaza Mutuwa Ka Raba: Waiwayen Dangantakar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III Da Makaɗa Sa’idu Faru
Maƙala kan Marigayi Makaɗa Sa’idu Faru ta ginu domin shiga sahun marubuta maƙalu domin samar da kundin da ke ƙunshe da nazarin waƙoƙin Sa’idu Farun don karrama Mai’alfarma Sarkin M...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni cikin salo mabambanta, wato ta baka ko rubutacciya.Waƙoƙin baka da rubutattu hanya ce mai gamsarwa wajen isar da saƙo. A wannan maƙala, an y...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...

