Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

View through CrossRef
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sauraro. Da wannan ne ya sa fasihai kan dage su ga sun zaɓo salailan da za su dace da su, su kuma ba su dama su ga sun sace zuciyar masu sauraren su, domin ganin haƙarsu ta cim ma ruwa na neman samu karɓuwa ga abokan hulɗarsu. Salon jerin sarƙe (Parallelism) shi ne dabarar tsarawa da jera kalmomi ko jumloli iri guda a cikin ɗiyan waƙa da nufin jaddadawa ko ƙarfafawa ko nuna wata danganataka ko alaƙa a tsakanin gunduwoyin ɗiyan waƙa. Wannan maƙala ta ƙudiri aniyar zaƙulowa tare da nazartar salon jerin sarƙe daga cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, inda za a bi wasu ɗiyan waƙoƙnsa a nuna yadda ya sarrafa salon, ta hanyar jerowa da tsara kalmomi da jumloli iri guda ko masu alaƙa da juna domin ya isar da wani saƙo. Maƙalar ta ginu ne a kan nau’in bincike bi-sharhi, inda aka zaƙulo wasu waƙoƙin makaɗin waɗanda ake ganin suna ƙunshe da salon jerin sarƙe a cikinsu, sannan a warware yadda ya ƙunshe tunanin nasa ta hanyar yin sharhi ga ɗiyan waƙoƙin. Maƙalar ta tattara bayanan da ta yi amfani da su ne ta hanyar bibiyar tahirin makaɗin da sauraron waƙoƙinsa domin ganin an tace waɗanda suke ƙunshe da wannan salo a cikinsu. Sannan kuma aka juye su a takarda. A ƙarshe maƙalar ta tabbatar da harsashenta na cewa waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru cike suke da salailai mabambanta, wanda salon jerin sarƙe ɗaya ne daga cikinsu, inda ta tabbatar da hakan ta hanyar kawo misalai na yadda makaɗin ya sarrafa salon, tare da yin sharhi a kan ɗiyan waƙoƙin nasa.
Title: Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Description:
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sauraro.
Da wannan ne ya sa fasihai kan dage su ga sun zaɓo salailan da za su dace da su, su kuma ba su dama su ga sun sace zuciyar masu sauraren su, domin ganin haƙarsu ta cim ma ruwa na neman samu karɓuwa ga abokan hulɗarsu.
Salon jerin sarƙe (Parallelism) shi ne dabarar tsarawa da jera kalmomi ko jumloli iri guda a cikin ɗiyan waƙa da nufin jaddadawa ko ƙarfafawa ko nuna wata danganataka ko alaƙa a tsakanin gunduwoyin ɗiyan waƙa.
Wannan maƙala ta ƙudiri aniyar zaƙulowa tare da nazartar salon jerin sarƙe daga cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, inda za a bi wasu ɗiyan waƙoƙnsa a nuna yadda ya sarrafa salon, ta hanyar jerowa da tsara kalmomi da jumloli iri guda ko masu alaƙa da juna domin ya isar da wani saƙo.
Maƙalar ta ginu ne a kan nau’in bincike bi-sharhi, inda aka zaƙulo wasu waƙoƙin makaɗin waɗanda ake ganin suna ƙunshe da salon jerin sarƙe a cikinsu, sannan a warware yadda ya ƙunshe tunanin nasa ta hanyar yin sharhi ga ɗiyan waƙoƙin.
Maƙalar ta tattara bayanan da ta yi amfani da su ne ta hanyar bibiyar tahirin makaɗin da sauraron waƙoƙinsa domin ganin an tace waɗanda suke ƙunshe da wannan salo a cikinsu.
Sannan kuma aka juye su a takarda.
A ƙarshe maƙalar ta tabbatar da harsashenta na cewa waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru cike suke da salailai mabambanta, wanda salon jerin sarƙe ɗaya ne daga cikinsu, inda ta tabbatar da hakan ta hanyar kawo misalai na yadda makaɗin ya sarrafa salon, tare da yin sharhi a kan ɗiyan waƙoƙin nasa.

Related Results

Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Wannan maƙala ta karkata ne a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, musamman waɗanda ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Aikin an yi shi ne a kan al’ada domin ya fito da...
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa. Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru...
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Al’adun kyautata zamantakewa, al’adu ne masu ɗimbin yawa da har yau ba a ƙayyade su ba, da ma dai al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Don haka dukkan tsarin da al’ad...

Back to Top