Javascript must be enabled to continue!
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
View through CrossRef
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’o’in mawaƙa da makaɗa da dama, musamman a yankin Sakkwato da Zamfara da Kabi. Wannan yankin ciki yake da fitattun mawaƙa da makaɗa na fannonin rayuwa daban-daban. Misali akwai Ibrahim Narambaɗa da Salihu Jan kiɗi da Sa’idu Faru da Aliyu Dandawo da Sani Aliyu Dandawo da kuma Alhaji Abdun Inka Bakura da suka yi fice a waƙoƙin sarauta. A ɗayan ɓangaren kuwa akwai Alhaji Musa Dankwairo Maradun da ya shahara a waƙoƙin Jama’a, kazalika akwai Alhaji Dan’Anace da ya shahara a fagen waƙoƙin maza (Dambe). Amali Sububu kuwa ya yi fice ne a waƙoƙin noma. Basirar da waɗannan makaɗa da mawaƙa suke da ita ba ƙarama ba ce. Gane irin wannan basirar kuwa ba zai yiyu ba, sai an koma ga fahimtar yadda suke ƙulla zaren tunaninsu musamman ta amfani da salailai masu armashi da burgewa. Nazari ya yi nisa game da waƙoƙin waɗannan mawaƙa, sai dai ba a zurfafa bincike ba dangane da salon aiwatar da waƙoƙinsu a ɗaiɗaikun mataki, face kaɗan daga cikin manazarta da suka aiwatar da irin wannan nazari (Dankwairo, 2019). Maƙasudin wannan maƙala shi ne domin a yi nazarin irin yadda makaɗa Abdun Inka Bakura yake turke ɗiyan waƙoƙinsa da yabon nasaba da kuma duba yadda suka mamaye wasu daga cikin waƙoƙinsa. Dabarun da aka bi wajen gano hakan kuwa shi ne ta amfani da sauraren waƙoƙinsa da aka naɗa a kaset-kaset da C.D da kuma wayoyin zamani. Daga ƙarshe takardar ta tantance da kuma gano yadda yabon nasaba ya mamaye sauran salailai da ke cikin waƙoƙin Abdun Inka Bakura da yadda kutsen salon ke ƙara ƙawata waƙoƙinsa. Takardar ta gano cewa da za a cire yabon nasaba a cikin waƙoƙinsa, da waƙoƙinsa ba su sami gindin zama ba.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Description:
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu.
Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’o’in mawaƙa da makaɗa da dama, musamman a yankin Sakkwato da Zamfara da Kabi.
Wannan yankin ciki yake da fitattun mawaƙa da makaɗa na fannonin rayuwa daban-daban.
Misali akwai Ibrahim Narambaɗa da Salihu Jan kiɗi da Sa’idu Faru da Aliyu Dandawo da Sani Aliyu Dandawo da kuma Alhaji Abdun Inka Bakura da suka yi fice a waƙoƙin sarauta.
A ɗayan ɓangaren kuwa akwai Alhaji Musa Dankwairo Maradun da ya shahara a waƙoƙin Jama’a, kazalika akwai Alhaji Dan’Anace da ya shahara a fagen waƙoƙin maza (Dambe).
Amali Sububu kuwa ya yi fice ne a waƙoƙin noma.
Basirar da waɗannan makaɗa da mawaƙa suke da ita ba ƙarama ba ce.
Gane irin wannan basirar kuwa ba zai yiyu ba, sai an koma ga fahimtar yadda suke ƙulla zaren tunaninsu musamman ta amfani da salailai masu armashi da burgewa.
Nazari ya yi nisa game da waƙoƙin waɗannan mawaƙa, sai dai ba a zurfafa bincike ba dangane da salon aiwatar da waƙoƙinsu a ɗaiɗaikun mataki, face kaɗan daga cikin manazarta da suka aiwatar da irin wannan nazari (Dankwairo, 2019).
Maƙasudin wannan maƙala shi ne domin a yi nazarin irin yadda makaɗa Abdun Inka Bakura yake turke ɗiyan waƙoƙinsa da yabon nasaba da kuma duba yadda suka mamaye wasu daga cikin waƙoƙinsa.
Dabarun da aka bi wajen gano hakan kuwa shi ne ta amfani da sauraren waƙoƙinsa da aka naɗa a kaset-kaset da C.
D da kuma wayoyin zamani.
Daga ƙarshe takardar ta tantance da kuma gano yadda yabon nasaba ya mamaye sauran salailai da ke cikin waƙoƙin Abdun Inka Bakura da yadda kutsen salon ke ƙara ƙawata waƙoƙinsa.
Takardar ta gano cewa da za a cire yabon nasaba a cikin waƙoƙinsa, da waƙoƙinsa ba su sami gindin zama ba.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Keɓaɓɓun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Ƙwararru Ta Yariman Bakura
Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Keɓaɓɓun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Ƙwararru Ta Yariman Bakura
Karin harshe yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar sadarwa kamar yadda fassara ke da matuƙar muhimmnci a ɓangaren kiwon lafiya, musamman a karkara da ƙauyuka.Wani ...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...

