Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Keɓaɓɓun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Ƙwararru Ta Yariman Bakura

View through CrossRef
Karin harshe yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar sadarwa kamar yadda fassara ke da matuƙar muhimmnci a ɓangaren kiwon lafiya, musamman a karkara da ƙauyuka.Wani binciken da aka gudanar ya nuna kashi 77% na ma’aikata da marasa lafiya da ke zuwa Asibitin Ƙwararru ta Yariman Bakura sun fi son amfani da harshen Hausa wajen sadarwa tsakanin marar lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya a matakai mabambanta. Har wa yau, daga cikin kashi 77% ɗin kashi 44% sun fi amfani da karin harshen Zamfarci (Bashir & Umar sh. 38, 2024). Wannan dalilin ne ya sa aka yi ƙoƙarin fito da tasirin karin harshen Zamfarci wajen fassara keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da ke Gusau. An yi amfani da Ra’in Fassara ta La’akari da Karin Harshe, wanda Giles & Johnson (1979) ya yi amfani da shi a aikinsa inda ya nuna yadda ake samun bambancin fassara ta la’akari da karin harshe da kuma waɗanda ake yi wa fassara. Binciken ya gano cewa ana samun bambanci ta fannin fassarar wasu keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya da suka shafi likitancin mata da na ƙananan yara tsakanin daidaitacciyar Hausa da kuma karin harshen Zamfarci ta fuskar tsarin sauti da gundarin kalmomi. Bayan da aka zaƙulo wasu kalmomin kiwon lafiya, aka fassara su tare da bayyana yadda ake faɗin su a Zamfarci, an ba wa ƙwararrun likitoci Zamfarawa domin tantancewa da ba da shawara saboda samun ingantacciyar fassara cikin karin harshen Zamfarci. Sakamakon ya kawo jadawali bakwai na wasu keɓaɓbun kalmomin da suka shafi likitancin mata da ƙananan yara. Ana sa ran a ci gaba da zaƙulo wasu keɓaɓbun kalmomi na wasu sassan kiwon lafiya domin taskace su da samar da wani ƙaramin kundi ko ƙamus na keɓaɓbun kalmomin kiwon lafiya cikin daidaitacciyar Hausa da karin harshen Zamfarci domin ƙara inganta sadarwa musamman a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da sauran asisibitocin da ke cikin ƙasar da ake amfani da karin harshen Zamfarci.
Title: Tasirin Karin Harshen Zamfarci a Fassarar Keɓaɓɓun Kalmomin Kiwon Lafiya a Asibitin Ƙwararru Ta Yariman Bakura
Description:
Karin harshe yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar sadarwa kamar yadda fassara ke da matuƙar muhimmnci a ɓangaren kiwon lafiya, musamman a karkara da ƙauyuka.
Wani binciken da aka gudanar ya nuna kashi 77% na ma’aikata da marasa lafiya da ke zuwa Asibitin Ƙwararru ta Yariman Bakura sun fi son amfani da harshen Hausa wajen sadarwa tsakanin marar lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya a matakai mabambanta.
Har wa yau, daga cikin kashi 77% ɗin kashi 44% sun fi amfani da karin harshen Zamfarci (Bashir & Umar sh.
38, 2024).
Wannan dalilin ne ya sa aka yi ƙoƙarin fito da tasirin karin harshen Zamfarci wajen fassara keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da ke Gusau.
An yi amfani da Ra’in Fassara ta La’akari da Karin Harshe, wanda Giles & Johnson (1979) ya yi amfani da shi a aikinsa inda ya nuna yadda ake samun bambancin fassara ta la’akari da karin harshe da kuma waɗanda ake yi wa fassara.
Binciken ya gano cewa ana samun bambanci ta fannin fassarar wasu keɓaɓɓun kalmomin kiwon lafiya da suka shafi likitancin mata da na ƙananan yara tsakanin daidaitacciyar Hausa da kuma karin harshen Zamfarci ta fuskar tsarin sauti da gundarin kalmomi.
Bayan da aka zaƙulo wasu kalmomin kiwon lafiya, aka fassara su tare da bayyana yadda ake faɗin su a Zamfarci, an ba wa ƙwararrun likitoci Zamfarawa domin tantancewa da ba da shawara saboda samun ingantacciyar fassara cikin karin harshen Zamfarci.
Sakamakon ya kawo jadawali bakwai na wasu keɓaɓbun kalmomin da suka shafi likitancin mata da ƙananan yara.
Ana sa ran a ci gaba da zaƙulo wasu keɓaɓbun kalmomi na wasu sassan kiwon lafiya domin taskace su da samar da wani ƙaramin kundi ko ƙamus na keɓaɓbun kalmomin kiwon lafiya cikin daidaitacciyar Hausa da karin harshen Zamfarci domin ƙara inganta sadarwa musamman a asibitin ƙwararru ta Yariman Bakura da sauran asisibitocin da ke cikin ƙasar da ake amfani da karin harshen Zamfarci.

Related Results

WAƘOƘIN KASSU ZURMI MATSAYIN RUMBUN TSIMIN NAGARTATTUN KALMOMIN HAUSA
WAƘOƘIN KASSU ZURMI MATSAYIN RUMBUN TSIMIN NAGARTATTUN KALMOMIN HAUSA
Wannan takarda ta bayyana irin gudummuwar da wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi ke iya bayarwa wajen ƙirƙira, tattala da kuma adana kalmomin Hausa na fannoni daban daban na cigaba...
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa. Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru...
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’...
Danganatakar Karin Magana Da Tunanin Bahaushe: Tsokaci Daga Magana Jari Ce Na Abubakar Imam
Danganatakar Karin Magana Da Tunanin Bahaushe: Tsokaci Daga Magana Jari Ce Na Abubakar Imam
Ilimin hikimomin al’umma fage ne da ake nazarin tarihin tsofaffin kayan kimiyyar al’umma masu alaƙa da cigaban ɗanadam. ilimin hikimomin al’umma ya ƙunshi rassa da dama da suka haɗ...
Nazarin Sarrafa Harshe A Waƙar ANPP Ba Na Shakka Ta Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago
Nazarin Sarrafa Harshe A Waƙar ANPP Ba Na Shakka Ta Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago
Marubuta waƙoƙin siyasa na Hausa kan yi amfani da basirar da Allah ya yi musu wajen yin amfani da sarrafa harshe cikin hikima domin su jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa. Aminu Ib...
TARON KASA DA KASA A KAN RAYUWA DA WAKOKIN ALHAJI ABUBAKAR KASSU ZURMI
TARON KASA DA KASA A KAN RAYUWA DA WAKOKIN ALHAJI ABUBAKAR KASSU ZURMI
Wannan takarda ta binciko yadda al'ummar Hausawa ke kallon mai sata, ta hanyar yin nazarin wasu daga cikin wakokin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, a bangaren la'akari da tasirin al'ad...
Nazarin Sarrafa Harshe A Waƙar ANPP Ba Na Shakka Ta Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago
Nazarin Sarrafa Harshe A Waƙar ANPP Ba Na Shakka Ta Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago
A wannan takarda, an tattauna matsayin makaɗi ko mawaƙi a cikin al’ummar Hausawa. Sa’annan an yi ƙoƙarin waiwayen wasu daga cikin alƙaluman da tarihi ya naɗe a fagen faɗakarwa kan ...

Back to Top