Javascript must be enabled to continue!
Nazarin Sarrafa Harshe A Waƙar ANPP Ba Na Shakka Ta Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago
View through CrossRef
Marubuta waƙoƙin siyasa na Hausa kan yi amfani da basirar da Allah ya yi musu wajen yin amfani da sarrafa harshe cikin hikima domin su jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa. Aminu Ibrahim Ɗandago shi ma na ɗaya daga cikin irin waɗannann marubuta da Allah ya horewa wannan. A wannan nazari an kalli yadda marubucin ya yi amfani da dabarar sarrafa harshe a waƙar Ba Na Shakka ta ANPP. An ɗora wannan nazari bisa Mazahabar Abdulƙadir Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun hada da tattaunawa da marubucin an kuma samo matanin waƙar daga hannun marubucin kai tsaye a kuma rubace. A binciken kuma an gano marubucin ya yi mafani da dabarar sarrafa harshe ta hanyar aron kalmomin Ingilishi da Larabci da Fulatanci da kalmomin Hausa masu sabuwar ma’ana karin harshen Kananci da ƙari a cikin kalma da kuma maganganun hikima irinsu: karin Magana da habaici da kuma zambo. Gudunmawa da binciken ya bayar ita ce, ƙara bada haske ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci sarrafa harshe a rubutacciyar waƙa, musamman a ɓangaren waƙoƙin siyasa ta fannin adabin Hausa.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Nazarin Sarrafa Harshe A Waƙar ANPP Ba Na Shakka Ta Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago
Description:
Marubuta waƙoƙin siyasa na Hausa kan yi amfani da basirar da Allah ya yi musu wajen yin amfani da sarrafa harshe cikin hikima domin su jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa.
Aminu Ibrahim Ɗandago shi ma na ɗaya daga cikin irin waɗannann marubuta da Allah ya horewa wannan.
A wannan nazari an kalli yadda marubucin ya yi amfani da dabarar sarrafa harshe a waƙar Ba Na Shakka ta ANPP.
An ɗora wannan nazari bisa Mazahabar Abdulƙadir Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa.
Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun hada da tattaunawa da marubucin an kuma samo matanin waƙar daga hannun marubucin kai tsaye a kuma rubace.
A binciken kuma an gano marubucin ya yi mafani da dabarar sarrafa harshe ta hanyar aron kalmomin Ingilishi da Larabci da Fulatanci da kalmomin Hausa masu sabuwar ma’ana karin harshen Kananci da ƙari a cikin kalma da kuma maganganun hikima irinsu: karin Magana da habaici da kuma zambo.
Gudunmawa da binciken ya bayar ita ce, ƙara bada haske ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci sarrafa harshe a rubutacciyar waƙa, musamman a ɓangaren waƙoƙin siyasa ta fannin adabin Hausa.
Related Results
Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma
Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma
Waƙa kamar yadda masana suka yi ta ƙoƙarin bayyanawa zance ne da ya saɓa da zance na yau da kullum domin ita shiryayyiyar magana ce mai ƙunshe da saƙo wadda ake aiwatarwa cikin hik...
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Wannan nazari mai suna “Habaici Cikin Waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” ta Alhaji Garba Gashuwa. Babbar manufar nazarin ita ce fito da habaici ta hanyar zaƙulo ire-iren hikimomi da b...
SARRAFA HARSHE A WAƘOƘIN MAKAƊA KASSU ZURMI
SARRAFA HARSHE A WAƘOƘIN MAKAƊA KASSU ZURMI
Sarrafa harshe lamari ne mai ƙayatarwa da ke bayyana ƙwarewar harshe. Sanin harshe yana tattare da sanin nahawun harshe da yadda ake sarrafa shi. Makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi...
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa. Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru...
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Nazarin Sarrafa Harshe A Waƙar ANPP Ba Na Shakka Ta Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago
Nazarin Sarrafa Harshe A Waƙar ANPP Ba Na Shakka Ta Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago
A wannan takarda, an tattauna matsayin makaɗi ko mawaƙi a cikin al’ummar Hausawa. Sa’annan an yi ƙoƙarin waiwayen wasu daga cikin alƙaluman da tarihi ya naɗe a fagen faɗakarwa kan ...
Feedback from plant species change amplifies CO2 enhancement of grassland productivity
Feedback from plant species change amplifies CO2 enhancement of grassland productivity
AbstractDynamic global vegetation models simulate feedbacks of vegetation change on ecosystem processes, but direct, experimental evidence for feedbacks that result from atmospheri...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...

