Javascript must be enabled to continue!
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
View through CrossRef
Wannan nazari mai suna “Habaici Cikin Waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” ta Alhaji Garba Gashuwa. Babbar manufar nazarin ita ce fito da habaici ta hanyar zaƙulo ire-iren hikimomi da basirori da dabaru na sarrafa harshe da mawallafin ya yi amfani da su a cikin waƙar domin ya jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa. An kalli yadda marubucin ya yi amfani da dabarar sanya habaici a waƙar cikin hikima domin ya isar da saƙonsa. An ɗora wannan nazari a bisa mazahabar Abdulƙadir Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun haɗa da samo matanin waƙar daga hannun marubucin a kuma rubuce tare da tattaunawa da shi. A nazarin kuma an gano marubucin ya yi amfani da dabarar sarrafa harshe ta sanya habaici a cikin waƙar don ya mayar da martani ga abokin adawa. Gudunmawar da nazarin ya bayar ita ce zai zama jagora ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci habaici a rubutacciyar waƙa, musamman waƙoƙin siyasa a fannin adabin Hausa.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Description:
Wannan nazari mai suna “Habaici Cikin Waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” ta Alhaji Garba Gashuwa.
Babbar manufar nazarin ita ce fito da habaici ta hanyar zaƙulo ire-iren hikimomi da basirori da dabaru na sarrafa harshe da mawallafin ya yi amfani da su a cikin waƙar domin ya jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa.
An kalli yadda marubucin ya yi amfani da dabarar sanya habaici a waƙar cikin hikima domin ya isar da saƙonsa.
An ɗora wannan nazari a bisa mazahabar Abdulƙadir Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa.
Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun haɗa da samo matanin waƙar daga hannun marubucin a kuma rubuce tare da tattaunawa da shi.
A nazarin kuma an gano marubucin ya yi amfani da dabarar sarrafa harshe ta sanya habaici a cikin waƙar don ya mayar da martani ga abokin adawa.
Gudunmawar da nazarin ya bayar ita ce zai zama jagora ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci habaici a rubutacciyar waƙa, musamman waƙoƙin siyasa a fannin adabin Hausa.
Related Results
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma
Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma
Waƙa kamar yadda masana suka yi ta ƙoƙarin bayyanawa zance ne da ya saɓa da zance na yau da kullum domin ita shiryayyiyar magana ce mai ƙunshe da saƙo wadda ake aiwatarwa cikin hik...
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Wannan takarda ta yi nazarin salon da mawaƙi Kassu Zurmi yake amfani da shi ne a waƙarasa wajen bayar da labarin baka a cikin waƙoƙin da yake yi. Manufar takardar ne ta nazarci iri...
NAZARIN YALWAR MA’ANAR KALMOMI A CIKIN WAƘOƘIN KASSU ZURMI
NAZARIN YALWAR MA’ANAR KALMOMI A CIKIN WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Wannan takardar za ta mayar da hankali ne kan ilimin ma’anar kalmomi waɗannda suka shafi yalwar ma’ana a cikin waƙoƙi biyu na Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, waƙar Nomau na Magarya da...
Nazari Da Sharhin Waƙar Begen Annabi (S.A.W.) Ta Kabiru Yahaya Classic
Nazari Da Sharhin Waƙar Begen Annabi (S.A.W.) Ta Kabiru Yahaya Classic
Sunan maƙalar ‘Nazari da Sharhin Waƙar Begen Annabi (S.A.W.) ta Kabiru Yahaya Classic. A cikin maƙalar an yi sharhin babba da ƙananan saƙonni da waƙar ke ɗauke da su da suka haɗa d...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...

