Javascript must be enabled to continue!
Ƙididdigar Wakilin Suna a Waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa
View through CrossRef
Wakilin suna yana ɗaya daga cikin muhimman rukunnan nahawu, don kusan duk zancen da za a yi a rubuce ko a baka, sai an samu ɗaya daga cikin nau’o’insa. Don haka, manufar wannan takarda ita ce ta ƙididdige nau’o’i da kuma yawa ko adadin wakilan sunayen da suke cikin waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa. An gudanar da wannan nazari ta hanyar karanta waƙar domin fito da yawan nau’o’i da kuma ƙididdige adadin wakilan sunayen da suke cikinta. Sannan kuma, an gabatar da sakamakon wannan takarda ta hanyar amfani da taswirar kara-tsaye (bar chart) wajen ƙididdige wakilan sunayen da ke cikin waƙar. Takardar ta gano yadda marubucin waƙar ya yi amfani da wakilan sunaye guda casa’in da huɗu wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Binciken ya nuna cewa marubucin waƙar ya ambaci nau’in wakilin suna rakaɓau sau 23 a waƙar tasa. Sannan ya ambaci wakilin suna zagin aikatau sau (45). Ya kuma ambaci wakilin suna mallakau sau 15. Har wa yau, marubucin ya ambaci wakilin suna dogarau sau 4, haka shi ma wakilin suna gama-gari ya ambae shi sau 4a cikin waƙarsa. Har ila yau, marubucin ya yi amfani da wakilin suna nunau sau 2. Daga ƙarshe kuma, marubucin ya yi amfani da wakilin suna kaikaitau sau 1 rak a cikin waƙar tasa..
Title: Ƙididdigar Wakilin Suna a Waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa
Description:
Wakilin suna yana ɗaya daga cikin muhimman rukunnan nahawu, don kusan duk zancen da za a yi a rubuce ko a baka, sai an samu ɗaya daga cikin nau’o’insa.
Don haka, manufar wannan takarda ita ce ta ƙididdige nau’o’i da kuma yawa ko adadin wakilan sunayen da suke cikin waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa.
An gudanar da wannan nazari ta hanyar karanta waƙar domin fito da yawan nau’o’i da kuma ƙididdige adadin wakilan sunayen da suke cikinta.
Sannan kuma, an gabatar da sakamakon wannan takarda ta hanyar amfani da taswirar kara-tsaye (bar chart) wajen ƙididdige wakilan sunayen da ke cikin waƙar.
Takardar ta gano yadda marubucin waƙar ya yi amfani da wakilan sunaye guda casa’in da huɗu wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi.
Binciken ya nuna cewa marubucin waƙar ya ambaci nau’in wakilin suna rakaɓau sau 23 a waƙar tasa.
Sannan ya ambaci wakilin suna zagin aikatau sau (45).
Ya kuma ambaci wakilin suna mallakau sau 15.
Har wa yau, marubucin ya ambaci wakilin suna dogarau sau 4, haka shi ma wakilin suna gama-gari ya ambae shi sau 4a cikin waƙarsa.
Har ila yau, marubucin ya yi amfani da wakilin suna nunau sau 2.
Daga ƙarshe kuma, marubucin ya yi amfani da wakilin suna kaikaitau sau 1 rak a cikin waƙar tasa.
Related Results
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa. Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru...
Şarkı eğitiminde iletişim, dil ve kültür
Şarkı eğitiminde iletişim, dil ve kültür
Bu araştırmada ses eğitimcilerinin iletişim bilgi ve becerileri ile estetik ve artistik tutumları incelenerek, dil ve kültür bilgilerini, duygu ve düşüncelerini öğrenciye sunma şek...
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Wannan nazari mai suna “Habaici Cikin Waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” ta Alhaji Garba Gashuwa. Babbar manufar nazarin ita ce fito da habaici ta hanyar zaƙulo ire-iren hikimomi da b...
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Wannan takarda ta yi nazarin salon da mawaƙi Kassu Zurmi yake amfani da shi ne a waƙarasa wajen bayar da labarin baka a cikin waƙoƙin da yake yi. Manufar takardar ne ta nazarci iri...
SUNCT and SUNA, Distinct Disorders or Spectrum of a Single Clinical Entity? A Meta-analysis
SUNCT and SUNA, Distinct Disorders or Spectrum of a Single Clinical Entity? A Meta-analysis
ABSTRACT
This study aimed to evaluate and compare the relative frequencies of clinical features between SUNCT and SUNA. Recently, many researcher...
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni cikin salo mabambanta, wato ta baka ko rubutacciya.Waƙoƙin baka da rubutattu hanya ce mai gamsarwa wajen isar da saƙo. A wannan maƙala, an y...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...
Kwatanta Tubalan Gina Turken Waƙar ‘Hauwa Maituwo ta Mamman Shata Katsina da ta Tafada Mai Tuwo ta Mamman Gawo Filinge
Kwatanta Tubalan Gina Turken Waƙar ‘Hauwa Maituwo ta Mamman Shata Katsina da ta Tafada Mai Tuwo ta Mamman Gawo Filinge
Wannan bincike an aiwatar da shi a kan waƙoƙin fitattun mawaƙan Hausa guda biyu (Mamman Shata Katsina na Nijeriya da Mamman Gawo Filinge na Jamhuriyar Nijar). Waƙar Mamman Shata da...

