Javascript must be enabled to continue!
Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma
View through CrossRef
Waƙa kamar yadda masana suka yi ta ƙoƙarin bayyanawa zance ne da ya saɓa da zance na yau da kullum domin ita shiryayyiyar magana ce mai ƙunshe da saƙo wadda ake aiwatarwa cikin hikima da balagar harshe ta hanyar zaɓen kalmomi da shirya su tare da sadar da su a kan wasu ƙa’idoji. Salo a cikin ayyukan adabi yakan kasance wata gada ce wadda ta kanta ne fasihi ke bi ya gwada ƙwanjin fasaharsa da baiwarsa ta mallakar harshe tare da samun damar isar da saƙonsa cikin sauƙi da burgewa. Masana irin su Leech (1968) da Yahaya (2001) da Garba (2014) sun tabbatar da cewa iya sarrafa salon fasihi shi zai ba shi dama ya samar da waƙa mai daɗi da armashi kuma har mutane su kwaɗaitu da waƙar tasa. Masana irin su Mukhtar (2001) da Yahaya (2001) da Adamu (2002) suna kallon salo a matsayin wani faffaɗan fage na nazari wanda kusan a iya cewa ba shi da iyaka amma duk da haka ana nazarinsa ta fuskar harshe da kuma adabi.Wannan maƙala ta yi nazarin yadda Alhaji Sani Sabulu Kanoma ya sarrafa salailai mabambanta ne a cikin waƙarsa ta ‘Salo’ musamman ta fuskar adabi, domin kuwa ba ta taɓo abin da ya shafi harshe ba. Maƙalar ta yi dubi ne na ƙwaƙƙwafi tare da ƙwanƙance ɗiyan waƙar da ƙoƙarin fayyace su a kan wani nau’i na salo. A wajen tattaro bayanai, maƙalar ta juyi wannan waƙa ta ‘Salo’ a rubuce, sannan ta bibiyi bayanan masana a kan salo da hanyoyin nazarinsa waɗanda suka zamar mata matashiya wajen ganin an zaƙulo nau’o’in salalai da makaɗin ya sarrafa a cikin waƙar. A ƙarshe maƙalar ta tabbatar da cewa makaɗin gwani ne wajen iya sarrafa salo wanda hakan ya sa waƙoƙinsa suka samu karɓuwa a wurin mutane kuma har duniya ta sansa a matsayin fitaccen makaɗi mai ɗimbin hikima sannan kuma waƙoƙin nasa suka ɗauki tsawon lokaci ana sauraren su ba tare da sun ɓace ba duk kuwa da cewa makaɗin ya daɗe da barin duniya.
Title: Salo Ruhin Waƙa: Nazarin Salo a Waƙar ‘Salo’ Ta Alhaji Sani Sabulu Kanoma
Description:
Waƙa kamar yadda masana suka yi ta ƙoƙarin bayyanawa zance ne da ya saɓa da zance na yau da kullum domin ita shiryayyiyar magana ce mai ƙunshe da saƙo wadda ake aiwatarwa cikin hikima da balagar harshe ta hanyar zaɓen kalmomi da shirya su tare da sadar da su a kan wasu ƙa’idoji.
Salo a cikin ayyukan adabi yakan kasance wata gada ce wadda ta kanta ne fasihi ke bi ya gwada ƙwanjin fasaharsa da baiwarsa ta mallakar harshe tare da samun damar isar da saƙonsa cikin sauƙi da burgewa.
Masana irin su Leech (1968) da Yahaya (2001) da Garba (2014) sun tabbatar da cewa iya sarrafa salon fasihi shi zai ba shi dama ya samar da waƙa mai daɗi da armashi kuma har mutane su kwaɗaitu da waƙar tasa.
Masana irin su Mukhtar (2001) da Yahaya (2001) da Adamu (2002) suna kallon salo a matsayin wani faffaɗan fage na nazari wanda kusan a iya cewa ba shi da iyaka amma duk da haka ana nazarinsa ta fuskar harshe da kuma adabi.
Wannan maƙala ta yi nazarin yadda Alhaji Sani Sabulu Kanoma ya sarrafa salailai mabambanta ne a cikin waƙarsa ta ‘Salo’ musamman ta fuskar adabi, domin kuwa ba ta taɓo abin da ya shafi harshe ba.
Maƙalar ta yi dubi ne na ƙwaƙƙwafi tare da ƙwanƙance ɗiyan waƙar da ƙoƙarin fayyace su a kan wani nau’i na salo.
A wajen tattaro bayanai, maƙalar ta juyi wannan waƙa ta ‘Salo’ a rubuce, sannan ta bibiyi bayanan masana a kan salo da hanyoyin nazarinsa waɗanda suka zamar mata matashiya wajen ganin an zaƙulo nau’o’in salalai da makaɗin ya sarrafa a cikin waƙar.
A ƙarshe maƙalar ta tabbatar da cewa makaɗin gwani ne wajen iya sarrafa salo wanda hakan ya sa waƙoƙinsa suka samu karɓuwa a wurin mutane kuma har duniya ta sansa a matsayin fitaccen makaɗi mai ɗimbin hikima sannan kuma waƙoƙin nasa suka ɗauki tsawon lokaci ana sauraren su ba tare da sun ɓace ba duk kuwa da cewa makaɗin ya daɗe da barin duniya.
Related Results
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su
wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Wannan nazari mai suna “Habaici Cikin Waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” ta Alhaji Garba Gashuwa. Babbar manufar nazarin ita ce fito da habaici ta hanyar zaƙulo ire-iren hikimomi da b...
Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Makaɗan baka na Hausa sun karkasu dangane da rukunan mutanen da suke yi wa kiɗa da waƙa. Waɗannan rabe-rabe na makaɗan baka sun haɗa da makaɗan fada-wato waɗanda suke yi wa fadar s...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Wannan takarda ta yi nazarin salon da mawaƙi Kassu Zurmi yake amfani da shi ne a waƙarasa wajen bayar da labarin baka a cikin waƙoƙin da yake yi. Manufar takardar ne ta nazarci iri...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...

