Javascript must be enabled to continue!
Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
View through CrossRef
Makaɗan baka na Hausa sun karkasu dangane da rukunan mutanen da suke yi wa kiɗa da waƙa. Waɗannan rabe-rabe na makaɗan baka sun haɗa da makaɗan fada-wato waɗanda suke yi wa fadar sarauta da jami’anta kiɗa da waƙa. Sai kuma makaɗan game-gari, waɗanda suke yi wa sauran jama’a kiɗa da waƙa. Wannan kasona makaɗan game-gari ya haɗa da makaɗan attajirai da masu sana’a da ‘yan siyasa da makaɗan bandariya da na bege da sauransu. Dukkanin waɗannan makaɗa suna amfani da dabarun jawo hankali domin isar da saƙonsu cikin sauƙi da burgewa ga jama’a. Sukan yi hakan ne kuwa domin kwarzanta wanda suke yi wa kiɗa da waƙa, a ɗaya ɓangaren kuma su kushe abokan adawar waɗanda suke wa waƙar. Irin waɗannan dabarun jawo hankali sun haɗa da: kwatantawa wadda ta ƙunshi kamantawa da siffantawa da kuma jinsintarwa. Haka kuma makaɗan sukan yi amfani da dabbantarwa da alamtarwa da sauran dabarun jawo hankali. Wannan takarda ta taƙaita ne ga nazarin siffantawa a cikin waƙar ‘Yandotan Tsahe ta Alhaji Musa Ɗankwairo. Manufar wannan takarda ita ce, bin diddigi tare da bayyana wuraren da Ɗankwairo ya yi amfani da siffantawa a cikin wannan waƙa da kuma hikimomin da suke tattare da yin hakan. Hanyoyin nema da tattara bayanan bincike su ne sauraron waƙoƙin Ɗanƙwairo a faya-fayan C.D da sauran su.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Description:
Makaɗan baka na Hausa sun karkasu dangane da rukunan mutanen da suke yi wa kiɗa da waƙa.
Waɗannan rabe-rabe na makaɗan baka sun haɗa da makaɗan fada-wato waɗanda suke yi wa fadar sarauta da jami’anta kiɗa da waƙa.
Sai kuma makaɗan game-gari, waɗanda suke yi wa sauran jama’a kiɗa da waƙa.
Wannan kasona makaɗan game-gari ya haɗa da makaɗan attajirai da masu sana’a da ‘yan siyasa da makaɗan bandariya da na bege da sauransu.
Dukkanin waɗannan makaɗa suna amfani da dabarun jawo hankali domin isar da saƙonsu cikin sauƙi da burgewa ga jama’a.
Sukan yi hakan ne kuwa domin kwarzanta wanda suke yi wa kiɗa da waƙa, a ɗaya ɓangaren kuma su kushe abokan adawar waɗanda suke wa waƙar.
Irin waɗannan dabarun jawo hankali sun haɗa da: kwatantawa wadda ta ƙunshi kamantawa da siffantawa da kuma jinsintarwa.
Haka kuma makaɗan sukan yi amfani da dabbantarwa da alamtarwa da sauran dabarun jawo hankali.
Wannan takarda ta taƙaita ne ga nazarin siffantawa a cikin waƙar ‘Yandotan Tsahe ta Alhaji Musa Ɗankwairo.
Manufar wannan takarda ita ce, bin diddigi tare da bayyana wuraren da Ɗankwairo ya yi amfani da siffantawa a cikin wannan waƙa da kuma hikimomin da suke tattare da yin hakan.
Hanyoyin nema da tattara bayanan bincike su ne sauraron waƙoƙin Ɗanƙwairo a faya-fayan C.
D da sauran su.
Related Results
Dabarun Jan Hankali A Waƙoƙin Baka: Nazari A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Dabarun Jan Hankali A Waƙoƙin Baka: Nazari A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Waƙoƙin baka na Hausa cike suke da dabarun jawo hankali. Wannan ya sa a kodayaushe za a ga waƙoƙin suna cike da armashi da salo mai ban-sha'awa. Gusau (2003 da 2023) ya kir...
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa
Wannan nazari mai suna “Habaici Cikin Waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” ta Alhaji Garba Gashuwa. Babbar manufar nazarin ita ce fito da habaici ta hanyar zaƙulo ire-iren hikimomi da b...
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musam...
Dabarun Bayar Da Labari: Nazari A Magana Jari Ce
Dabarun Bayar Da Labari: Nazari A Magana Jari Ce
Dabarun bayar da labari dabara ce da mawari ke amfani da ita wajen warware labarinsa. Warwara kuwa mawari shi ne yake da dama wajen nuna ƙwarewarsa domin jan zarensa sala-sala ta y...
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Salon Bayar da Labarin Baka a Waƙar Kassu Zurmi ta Sarkin Gabas Usman Jikan Hassan
Wannan takarda ta yi nazarin salon da mawaƙi Kassu Zurmi yake amfani da shi ne a waƙarasa wajen bayar da labarin baka a cikin waƙoƙin da yake yi. Manufar takardar ne ta nazarci iri...
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa. Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru...
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’...
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi d...

