Javascript must be enabled to continue!
Tubalin Yabon Mata a Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo
View through CrossRef
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da matsayin mata a wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo ta sigar yabo. Dalilin da ya sa mutane ba su yi rubutu sosai ba, saboda hankali bai koma kai ba. Akwai wani ilimi a ɓoye, wanda makaɗa suke bijiro da shi, wanda in an yi nazarin sa za a samu ƙaruwa wajen rubutun yau da kullum. Don rayuwar al’umma da sauran su a fagen nazari. An ɗora wannan binciken a kan ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) wadda Gusau (2015) ya assasa. Wanda yake Magana musamman a kan sanin sunan makaɗi da tarihinsa da kuma ayyana tubulin ginin turke, kamar yadda aka kawo cikin wannan nazari. A wajen tattara bayanai an yi amfani da hanyoyi mabambanta kamar sauraren kaset-kaset na waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo, musamman waɗanda aka nazarta, da kuma duba littattafai da kundayen bincike da maƙalu da kuma tattaunawa da masana waƙoƙin baka na Hausa domin samun bayanan da suka zama fitila ga nazarin. Daga ƙarshe sakamakon bincike ya nuna cewa, Alhaji Musa Ɗanƙwairo yana amfani da tubalan yabon mata a wasu waƙoƙinsa.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Tubalin Yabon Mata a Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo
Description:
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da matsayin mata a wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo ta sigar yabo.
Dalilin da ya sa mutane ba su yi rubutu sosai ba, saboda hankali bai koma kai ba.
Akwai wani ilimi a ɓoye, wanda makaɗa suke bijiro da shi, wanda in an yi nazarin sa za a samu ƙaruwa wajen rubutun yau da kullum.
Don rayuwar al’umma da sauran su a fagen nazari.
An ɗora wannan binciken a kan ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) wadda Gusau (2015) ya assasa.
Wanda yake Magana musamman a kan sanin sunan makaɗi da tarihinsa da kuma ayyana tubulin ginin turke, kamar yadda aka kawo cikin wannan nazari.
A wajen tattara bayanai an yi amfani da hanyoyi mabambanta kamar sauraren kaset-kaset na waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo, musamman waɗanda aka nazarta, da kuma duba littattafai da kundayen bincike da maƙalu da kuma tattaunawa da masana waƙoƙin baka na Hausa domin samun bayanan da suka zama fitila ga nazarin.
Daga ƙarshe sakamakon bincike ya nuna cewa, Alhaji Musa Ɗanƙwairo yana amfani da tubalan yabon mata a wasu waƙoƙinsa.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Waƙoƙin yara mata da ‘yammata wani babban rukuni ne a al’adar Hausawa. Waƙoƙi ne da ake yi domin samun nishaɗi da tarbiyya da ilmantarwa da kuma gargaɗi ga ‘yammata tun suna ƙanana...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Tubalan Gina Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi
Tubalan Gina Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi
Wannan takarda za ta bi sawun wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi da ya rera domin fito da tubalan gina wasu daga cikin waƙoƙinsa. Hanyoyin da aka bi wajen a...
Mata Makusantan ‘Yan Tauri A Bakin Makaɗa Kassu Zurmi
Mata Makusantan ‘Yan Tauri A Bakin Makaɗa Kassu Zurmi
Wannan maƙala tana magana a kan matsayi da alaƙar jinsin mata a sana’ar tauri da ‘yan tauri, tare da wasu taurari da suka fito a waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi. Bincike ya fahimci cewa...

