Javascript must be enabled to continue!
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
View through CrossRef
Waƙoƙin yara mata da ‘yammata wani babban rukuni ne a al’adar Hausawa. Waƙoƙi ne da ake yi domin samun nishaɗi da tarbiyya da ilmantarwa da kuma gargaɗi ga ‘yammata tun suna ƙanana. Waƙoƙin suna ƙunshe da darussa masu muhimmanci da suka shafi rayuwa da ladabi da tsaftace hulɗa da sauran mutane, ko dogaro da kai ta hanyar sana’o’i. An ƙudiri aniyar yin wannan bincike ne ganin yadda a yanzu ire-iren waɗannan waƙoƙi masu ƙima suka tafi hanyar ɓacewa kuma waƙoƙin fiyano na ƙoƙarin maye gurbinsu. Daga cikin manufofin waɗannan waƙoƙi na yara mata akwai koyar da tarbiyya da waɗanda ke ilimantarwa, ga waɗanda ake yi domin tallata sana’o’i, akwai waɗanda ake shiryarwa ga rayuwar aure da kuma waɗanda ake yi domin nishaɗantarwa. Na ɗora wannan bincike a kan ra’in Adabin Gargajiya (Folklore Theory) wanda William John Thoms ya ƙirƙira a shekarar 1846 daga baya kuma Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo ya kafa ƙa’idojin nazarin waƙoƙin gargajiya daga 1970 har zuwa lokacin da muke yanzu. Ra’in Adabin Gargajiya yana nazari a kan abubuwan da al’umma ke gadonsu ta baka. Don haka, waƙoƙin yara mata tubala ne da suka fito daga al’ada waɗanda ake gado daga iyaye zuwa yara cikin sauƙi da nishaɗi, kuma waƙoƙin ba don wasa kawai ake yi ba, al’adu ne waɗanda ke shiryar da ‘yammata a kan yadda za su taso cikin ladabi da tarbiyya. Hanyoyin da aka bi domin samun sahihan bayanai na wannan bincike sun haɗa da nazartar littatafai da suka zo hannu masu alaƙa da aikin da sauraro da naɗar wasu waƙoƙi daga waɗanda abin ya shafa, an yi amfani da wayar hannu domin naɗar waƙoƙin. Haka kuma an samu misalan wasu waƙoƙin daga marubuciyar. Sakamakon da aka samu bayan gudanar da wannan bincike sun haɗa da duk da sauye-sauyen da aka samu na zamani waƙoƙin yara da ‘yammata sun ci gaba da zama wata hanya mai tasiri wadda al’umma ke amfani da ita wajen gina tunanin yara da shirya su domin rayuwar gaba. Wannan ya nuna cewa waƙoƙin ba wai ana yin su ne kawai don nishaɗi ba, suna taka muhimmiyar rawa wajen tsare al’ada da haɓaka ilimi.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Description:
Waƙoƙin yara mata da ‘yammata wani babban rukuni ne a al’adar Hausawa.
Waƙoƙi ne da ake yi domin samun nishaɗi da tarbiyya da ilmantarwa da kuma gargaɗi ga ‘yammata tun suna ƙanana.
Waƙoƙin suna ƙunshe da darussa masu muhimmanci da suka shafi rayuwa da ladabi da tsaftace hulɗa da sauran mutane, ko dogaro da kai ta hanyar sana’o’i.
An ƙudiri aniyar yin wannan bincike ne ganin yadda a yanzu ire-iren waɗannan waƙoƙi masu ƙima suka tafi hanyar ɓacewa kuma waƙoƙin fiyano na ƙoƙarin maye gurbinsu.
Daga cikin manufofin waɗannan waƙoƙi na yara mata akwai koyar da tarbiyya da waɗanda ke ilimantarwa, ga waɗanda ake yi domin tallata sana’o’i, akwai waɗanda ake shiryarwa ga rayuwar aure da kuma waɗanda ake yi domin nishaɗantarwa.
Na ɗora wannan bincike a kan ra’in Adabin Gargajiya (Folklore Theory) wanda William John Thoms ya ƙirƙira a shekarar 1846 daga baya kuma Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo ya kafa ƙa’idojin nazarin waƙoƙin gargajiya daga 1970 har zuwa lokacin da muke yanzu.
Ra’in Adabin Gargajiya yana nazari a kan abubuwan da al’umma ke gadonsu ta baka.
Don haka, waƙoƙin yara mata tubala ne da suka fito daga al’ada waɗanda ake gado daga iyaye zuwa yara cikin sauƙi da nishaɗi, kuma waƙoƙin ba don wasa kawai ake yi ba, al’adu ne waɗanda ke shiryar da ‘yammata a kan yadda za su taso cikin ladabi da tarbiyya.
Hanyoyin da aka bi domin samun sahihan bayanai na wannan bincike sun haɗa da nazartar littatafai da suka zo hannu masu alaƙa da aikin da sauraro da naɗar wasu waƙoƙi daga waɗanda abin ya shafa, an yi amfani da wayar hannu domin naɗar waƙoƙin.
Haka kuma an samu misalan wasu waƙoƙin daga marubuciyar.
Sakamakon da aka samu bayan gudanar da wannan bincike sun haɗa da duk da sauye-sauyen da aka samu na zamani waƙoƙin yara da ‘yammata sun ci gaba da zama wata hanya mai tasiri wadda al’umma ke amfani da ita wajen gina tunanin yara da shirya su domin rayuwar gaba.
Wannan ya nuna cewa waƙoƙin ba wai ana yin su ne kawai don nishaɗi ba, suna taka muhimmiyar rawa wajen tsare al’ada da haɓaka ilimi.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Gurbin Musulunci A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Gurbin Musulunci A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙan Hausa mutane ne da Allah ya yi wa baiwa da basira da hikimomi wajen tsara zantuttukan hikima a cikin baitocin waƙa ko ɗiyan waƙa. Wannan baiwa da Allah ya yi musu ya sa ake...
Gurbin Sana’o’in Gargajiyar Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Gurbin Sana’o’in Gargajiyar Hausawa a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Babbar manufar maƙalar ita ce fito da sana’o’in gargajiya na Hausawa, waɗanda Kassu Zurmi ya taskace a cikin waƙoƙinsa tare da duban yadda shi makaɗin ya kalle su a cikin waƙoƙinsa...
Yara Bakımında Kullanılan Pansuman Materyalleri
Yara Bakımında Kullanılan Pansuman Materyalleri
Yara bakımında yaklaşımlar ve uygulamalar geçmişten günümüze hızla gelişmiştir. Yara bakımının hedefleri en kısa sürede doku onarımı sağlamak, bozulan anatomik veya fonksiyonel dur...
Geç İyileşen Yara ve Enfeksiyon Bölgelerinde Uygulanan Kitosan Temelli Gümüş Nanopartikül ve İlaç İçeren Hidrojel Yara Örtüleri
Geç İyileşen Yara ve Enfeksiyon Bölgelerinde Uygulanan Kitosan Temelli Gümüş Nanopartikül ve İlaç İçeren Hidrojel Yara Örtüleri
Yara, doku ya da organ bütünlüğünde gerçekleşmiş olan bir bozulmadır. Yara türleri akut ve kronik yara şeklinde sınıflandırılmaktadır. Akut yaralar iyileşmeye iyi yanıt verirken kr...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

