Javascript must be enabled to continue!
SARRAFA HARSHE A WAƘOƘIN MAKAƊA KASSU ZURMI
View through CrossRef
Sarrafa harshe lamari ne mai ƙayatarwa da ke bayyana ƙwarewar harshe. Sanin harshe yana tattare da sanin nahawun harshe da yadda ake sarrafa shi. Makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi fitaccen makaɗin maza ne da yake da baiwa ta waƙa. Manufar wannan maƙala ita ce fito da sarrafa harshe da makaɗa Kassu ya yi a cikin wasu waƙoƙinsa, tare da fayyace su da misalansu domin ganin yadda sarrafa harshe yake. Maƙalar za ta yi amfani da dukkan hanyoyin biyu na bicike wato manya da ƙananan hanyoyi. A cikin hanyoyin kuwa za a yi hrarraki da karance-karancen kundaye da mujallu da litattafai duk domin samun wata gudummuwa da za ta gina wannan maƙala. Za a kuma yi amfani da hanyar ɗora aiki ta amfani da karin maganar Hausawa mai cewa “ɗan na iya wanda ya fi ɗan na koya”. Sakamakon wannan maƙala ya gano cewa makaɗa Kassu tantagaryar Bahaushe ne wanda ya naƙalci harshen Hausa kuma yake sarrafa shi a cikin mafi yawan waƙoƙinsa.
Title: SARRAFA HARSHE A WAƘOƘIN MAKAƊA KASSU ZURMI
Description:
Sarrafa harshe lamari ne mai ƙayatarwa da ke bayyana ƙwarewar harshe.
Sanin harshe yana tattare da sanin nahawun harshe da yadda ake sarrafa shi.
Makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi fitaccen makaɗin maza ne da yake da baiwa ta waƙa.
Manufar wannan maƙala ita ce fito da sarrafa harshe da makaɗa Kassu ya yi a cikin wasu waƙoƙinsa, tare da fayyace su da misalansu domin ganin yadda sarrafa harshe yake.
Maƙalar za ta yi amfani da dukkan hanyoyin biyu na bicike wato manya da ƙananan hanyoyi.
A cikin hanyoyin kuwa za a yi hrarraki da karance-karancen kundaye da mujallu da litattafai duk domin samun wata gudummuwa da za ta gina wannan maƙala.
Za a kuma yi amfani da hanyar ɗora aiki ta amfani da karin maganar Hausawa mai cewa “ɗan na iya wanda ya fi ɗan na koya”.
Sakamakon wannan maƙala ya gano cewa makaɗa Kassu tantagaryar Bahaushe ne wanda ya naƙalci harshen Hausa kuma yake sarrafa shi a cikin mafi yawan waƙoƙinsa.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Makaɗa suna amfani da wani nao’in salo da ake kira salon dibilwa, a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani salo ne na nuna gwanintar harshe da ƙwarewa ta yadda sukan kawo wata kalma da a...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...