Javascript must be enabled to continue!
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
View through CrossRef
Makaɗa suna amfani da wani nao’in salo da ake kira salon dibilwa, a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani salo ne na nuna gwanintar harshe da ƙwarewa ta yadda sukan kawo wata kalma da a zahiri ba ma’anarta suke nufi ba, sai su bar mai sauraron waƙar ya samar ma kansa mafita ta hanyar gano manufar, ko kuma su kawo waso zantuttukan azancin Magana wanda sai mai sauraro ya yi nasa ƙoƙarin sannan zai fahimci manufarsu. Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi gwani ne wajen amfani da wannan salon a cikin waƙoƙinsa, don haka ne wannan muƙalar ta yi nazarin yadda ya kawo shi a cikin waƙoƙin tare da sharhantawa don amfanin manazartan waƙoƙin Hausa. Manufar wannan muƙala ita ce yin nazarin kalaman dibilwa da azancin Magana a wasu waƙoƙin Kassu tare da bayyana sautukan da mawaƙin yake amfani da su domin ƙulla zaren tunaninsa. An yi amfani da dabarar sauraren waƙoƙimsa da nazarce-nazarcen masana a matsayin hanyoyin da aka bi domin tattara bayanan da aka yi amfani da su a wannan muƙala. A ƙoƙarin cimma manufa an yi amfani da mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya wacce ta bayyana hanyoyin da ake nazarin yadda ake nazarin waƙar baka bahaushiya (WBB). Wanda ya jagoranci wannan mazhabar shi ne Farfesa Sa’id Muhammad Gusau. Bayan kammala wannan muƙala, an an lura da da cewa Makaɗa Kassu Zurmi yana amfani da salon dibilwa da azancin Magana don nuna gwanintar harshe da kuma yin waskiya a cikin waƙoƙinsa. Zaɓaɓɓun kalmomi: Titif. ɗamrin baki, rimis, ‘Yan nalutsa, tara.
Sokoto State University
Title: Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Description:
Makaɗa suna amfani da wani nao’in salo da ake kira salon dibilwa, a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani salo ne na nuna gwanintar harshe da ƙwarewa ta yadda sukan kawo wata kalma da a zahiri ba ma’anarta suke nufi ba, sai su bar mai sauraron waƙar ya samar ma kansa mafita ta hanyar gano manufar, ko kuma su kawo waso zantuttukan azancin Magana wanda sai mai sauraro ya yi nasa ƙoƙarin sannan zai fahimci manufarsu.
Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi gwani ne wajen amfani da wannan salon a cikin waƙoƙinsa, don haka ne wannan muƙalar ta yi nazarin yadda ya kawo shi a cikin waƙoƙin tare da sharhantawa don amfanin manazartan waƙoƙin Hausa.
Manufar wannan muƙala ita ce yin nazarin kalaman dibilwa da azancin Magana a wasu waƙoƙin Kassu tare da bayyana sautukan da mawaƙin yake amfani da su domin ƙulla zaren tunaninsa.
An yi amfani da dabarar sauraren waƙoƙimsa da nazarce-nazarcen masana a matsayin hanyoyin da aka bi domin tattara bayanan da aka yi amfani da su a wannan muƙala.
A ƙoƙarin cimma manufa an yi amfani da mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya wacce ta bayyana hanyoyin da ake nazarin yadda ake nazarin waƙar baka bahaushiya (WBB).
Wanda ya jagoranci wannan mazhabar shi ne Farfesa Sa’id Muhammad Gusau.
Bayan kammala wannan muƙala, an an lura da da cewa Makaɗa Kassu Zurmi yana amfani da salon dibilwa da azancin Magana don nuna gwanintar harshe da kuma yin waskiya a cikin waƙoƙinsa.
Zaɓaɓɓun kalmomi: Titif.
ɗamrin baki, rimis, ‘Yan nalutsa, tara.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...

