Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

WAƘOƘIN KASSU ZURMI MATSAYIN RUMBUN TSIMIN NAGARTATTUN KALMOMIN HAUSA

View through CrossRef
Wannan takarda ta bayyana irin gudummuwar da wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi ke iya bayarwa wajen ƙirƙira, tattala da kuma adana kalmomin Hausa na fannoni daban daban na cigaban al’uma kamar su : fannin noma, tarbiya, mu’amala, wasanni, jarumataka, ds. Tattara kalmomin wanɗannan fannonin, da ma wasunsu, ta hayar kalato su daga cikin wasu daga waƙoƙin na Zurmi, da kuma fassara su zuwa harshen Faransanci kan iya taikamawa wajen bunƙasa ilimi, musamman a ƙasar da Hausa ke cigaba da fuskantar mallaka da kakagida na wasu harsunan Turai. Manufar wannan bincike ita ce, ƙoto kalmomin fannu daga waƙoƙin Kassu Zurmi ta hanyar rubuta su bisa bin umurnin ƙudirin dokar rubutun daidaitacciyar Hausa mai lamba 212 na 19 ga watan Oktoba 1999 na ofishin Ministan ilimi na Jamhuriyar Nijar. Sakamakon binciken zai taimaka sosai da muhimman kalmomi don amfani da su a fannoni daban-daban. Keɓaɓɓun kalmomi : Boda, waƙoƙin Kassu Zurmi, rumbun tsimin, kalmomin fannu, Hausa, Faransanci.
Title: WAƘOƘIN KASSU ZURMI MATSAYIN RUMBUN TSIMIN NAGARTATTUN KALMOMIN HAUSA
Description:
Wannan takarda ta bayyana irin gudummuwar da wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi ke iya bayarwa wajen ƙirƙira, tattala da kuma adana kalmomin Hausa na fannoni daban daban na cigaban al’uma kamar su : fannin noma, tarbiya, mu’amala, wasanni, jarumataka, ds.
Tattara kalmomin wanɗannan fannonin, da ma wasunsu, ta hayar kalato su daga cikin wasu daga waƙoƙin na Zurmi, da kuma fassara su zuwa harshen Faransanci kan iya taikamawa wajen bunƙasa ilimi, musamman a ƙasar da Hausa ke cigaba da fuskantar mallaka da kakagida na wasu harsunan Turai.
Manufar wannan bincike ita ce, ƙoto kalmomin fannu daga waƙoƙin Kassu Zurmi ta hanyar rubuta su bisa bin umurnin ƙudirin dokar rubutun daidaitacciyar Hausa mai lamba 212 na 19 ga watan Oktoba 1999 na ofishin Ministan ilimi na Jamhuriyar Nijar.
Sakamakon binciken zai taimaka sosai da muhimman kalmomi don amfani da su a fannoni daban-daban.
Keɓaɓɓun kalmomi : Boda, waƙoƙin Kassu Zurmi, rumbun tsimin, kalmomin fannu, Hausa, Faransanci.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...

Back to Top