Javascript must be enabled to continue!
Takalmin Kaza Mutuwa Ka Raba: Waiwayen Dangantakar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III Da Makaɗa Sa’idu Faru
View through CrossRef
Maƙala kan Marigayi Makaɗa Sa’idu Faru ta ginu domin shiga sahun marubuta maƙalu domin samar da kundin da ke ƙunshe da nazarin waƙoƙin Sa’idu Farun don karrama Mai’alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Macciɗo. Sa’idu Faru mawaƙin baka ne da ke cikin sahun jerin makaɗan bakan ƙasar Hausa. Sa’idu Faru mawaƙin rukunin Sarakunan ƙasar Hausa ne. Sauraren waƙoƙinsa ma sai manyan mutane musamman sarakuna, da jinin sarauta da waɗanda suke da dangantaka da fada da kuma manazarta ƙumshiyarsu, da neman tarihin abin da ya samar da waƙoƙin nasa. Fahimtar irin waɗannan abubuwan ne ya yunƙurar da azamar wannan maƙalar. Bayan an saurari tattaunawar da aka yi da shi lokacin da yake raye, da kuma wasu bayanai da masu gidansa Sarakai suka gabatar game da shi, sai na fahimci matsayin da ya bai wa kansa tare kuma da la’akari da yanayin matsayin da yake da shi a idon Sarakuna. Idan dai sarauta da waƙoƙin makaɗan sarauta a ƙasar Hausa za a yi nazari to babu wata tantama ba za a tsallake na Sa’idu Faru ba. Idan kuma shahararren fasihi mai zalaƙar baka ake nema, to Sa’idu shi ne kullume. Takalmin kaza mutu ka raba na nuni ne da irin zamantakewar ƙauna da ke akwai tsakanin basarake da baransa kamar yadda ya kasance tsakanin Sa’idu Faru da Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo.
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Takalmin Kaza Mutuwa Ka Raba: Waiwayen Dangantakar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III Da Makaɗa Sa’idu Faru
Description:
Maƙala kan Marigayi Makaɗa Sa’idu Faru ta ginu domin shiga sahun marubuta maƙalu domin samar da kundin da ke ƙunshe da nazarin waƙoƙin Sa’idu Farun don karrama Mai’alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Macciɗo.
Sa’idu Faru mawaƙin baka ne da ke cikin sahun jerin makaɗan bakan ƙasar Hausa.
Sa’idu Faru mawaƙin rukunin Sarakunan ƙasar Hausa ne.
Sauraren waƙoƙinsa ma sai manyan mutane musamman sarakuna, da jinin sarauta da waɗanda suke da dangantaka da fada da kuma manazarta ƙumshiyarsu, da neman tarihin abin da ya samar da waƙoƙin nasa.
Fahimtar irin waɗannan abubuwan ne ya yunƙurar da azamar wannan maƙalar.
Bayan an saurari tattaunawar da aka yi da shi lokacin da yake raye, da kuma wasu bayanai da masu gidansa Sarakai suka gabatar game da shi, sai na fahimci matsayin da ya bai wa kansa tare kuma da la’akari da yanayin matsayin da yake da shi a idon Sarakuna.
Idan dai sarauta da waƙoƙin makaɗan sarauta a ƙasar Hausa za a yi nazari to babu wata tantama ba za a tsallake na Sa’idu Faru ba.
Idan kuma shahararren fasihi mai zalaƙar baka ake nema, to Sa’idu shi ne kullume.
Takalmin kaza mutu ka raba na nuni ne da irin zamantakewar ƙauna da ke akwai tsakanin basarake da baransa kamar yadda ya kasance tsakanin Sa’idu Faru da Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo.
Related Results
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Jirwaye Mai Kama Da Wanka: Ɓirɓishin Kore a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru Na Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo
Wannan maƙala ta karkata ne a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, musamman waɗanda ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Aikin an yi shi ne a kan al’ada domin ya fito da...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris
Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni cikin salo mabambanta, wato ta baka ko rubutacciya.Waƙoƙin baka da rubutattu hanya ce mai gamsarwa wajen isar da saƙo. A wannan maƙala, an y...
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Sakkwatanci a Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Kana Shirye Baban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo
Faɗaɗa da bunƙasa da kuma nisantar juna ga masu magana da harshe, shi yake haifar da kare-karensa. Mawaƙa sukan yi amfani da karin harshensu a yayin rera waƙoƙi, makaɗa Sa’idu Faru...
Patients with History of Intravenous Drug Use (IDU) with Septic Arthritis of the Foot and Ankle Have Suboptimal Hospitalization Outcomes Compared to Patients Without IDU
Patients with History of Intravenous Drug Use (IDU) with Septic Arthritis of the Foot and Ankle Have Suboptimal Hospitalization Outcomes Compared to Patients Without IDU
Category:
Infection
Introduction/Purpose:
Although intravenous drug use (IDU) is a...
Sassan Waƙa ‘‘Ta Tsaru!’’ a ‘Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa’
Sassan Waƙa ‘‘Ta Tsaru!’’ a ‘Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa’
Tsakure: A gargajiyance, ta alƙalamin Sadaukin Shaihin Malami Abdulƙadir Ɗangambo, Hausawa kan hukumta waƙa da ɗayan matakai huɗu na yabo ko kushewa (Ɗangambo, 2007: 7-9). Wannan m...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Turken Nasaba a Cikin Wasu Waƙoƙin Abdun Inka Bakura
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’...

