Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Sassan Waƙa ‘‘Ta Tsaru!’’ a ‘Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa’

View through CrossRef
Tsakure: A gargajiyance, ta alƙalamin Sadaukin Shaihin Malami Abdulƙadir Ɗangambo, Hausawa kan hukumta waƙa da ɗayan matakai huɗu na yabo ko kushewa (Ɗangambo, 2007: 7-9). Wannan muƙala ta saka waƙar “Kana shire Baban ‘Yan Ruwa Na Bello Jikan ɗan Hodiyo” wadda Sa’idu Faru ya yi wa Alhaji Muhammadu Macciɗo, a mataki na ɗaya, kuma tun kafin ya zama Sarkin Musulmi. Muƙalar ta yi bayani cewa wannan waƙa ita ce za a iya yabawa da cewa “Ta tsaru” ko “Ta burge ni” ko a ce “Ta yi” ko kuma da “Habawa!”, da dai sauransu. Hujjar da aka kafa wannan iƙirari ita ce amfanin da Sa’idu Faru ya yi da sassa uku na waƙa waɗanda su ne jigo, da zubi da tsari, da salo, waɗanda kuma mabambanta ne a yadda mawaƙin ya yi amfani da su. A taƙaice sassan uku kowanensu iri-iri ne ba tilau-tilau ba. Su ne ake ganin muhimmai waɗanda suka sa waƙar ta hau mataki na ɗaya a idon Bahaushe a gargajiyance. Haka kuma mawaƙin ya tsara waƙar yana mai cusa wani sashi cikin wani ba tare da haddasa ruɗani ba.
Title: Sassan Waƙa ‘‘Ta Tsaru!’’ a ‘Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa’
Description:
Tsakure: A gargajiyance, ta alƙalamin Sadaukin Shaihin Malami Abdulƙadir Ɗangambo, Hausawa kan hukumta waƙa da ɗayan matakai huɗu na yabo ko kushewa (Ɗangambo, 2007: 7-9).
Wannan muƙala ta saka waƙar “Kana shire Baban ‘Yan Ruwa Na Bello Jikan ɗan Hodiyo” wadda Sa’idu Faru ya yi wa Alhaji Muhammadu Macciɗo, a mataki na ɗaya, kuma tun kafin ya zama Sarkin Musulmi.
Muƙalar ta yi bayani cewa wannan waƙa ita ce za a iya yabawa da cewa “Ta tsaru” ko “Ta burge ni” ko a ce “Ta yi” ko kuma da “Habawa!”, da dai sauransu.
Hujjar da aka kafa wannan iƙirari ita ce amfanin da Sa’idu Faru ya yi da sassa uku na waƙa waɗanda su ne jigo, da zubi da tsari, da salo, waɗanda kuma mabambanta ne a yadda mawaƙin ya yi amfani da su.
A taƙaice sassan uku kowanensu iri-iri ne ba tilau-tilau ba.
Su ne ake ganin muhimmai waɗanda suka sa waƙar ta hau mataki na ɗaya a idon Bahaushe a gargajiyance.
Haka kuma mawaƙin ya tsara waƙar yana mai cusa wani sashi cikin wani ba tare da haddasa ruɗani ba.

Related Results

Verb “kana
Verb “kana
This study addresses the verb “kana” in its confirmed form and it was not limited to what the grammarians mentioned in a few specific cases when “kana” is prefixed. It took a lot o...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...
‘Hard Yakka’: Living With a Disability in the West Kimberley
‘Hard Yakka’: Living With a Disability in the West Kimberley
<p>This report investigates the lived experiences of Aboriginal people with disabilities living in the West Kimberley region of Western Australia, covered by the local govern...

Hîkayeta Keyhana Frenk û Feqe Ehmedê Baban: Mirin Çêtir e ji Fîraqê
Hîkayeta Keyhana Frenk û Feqe Ehmedê Baban: Mirin Çêtir e ji Fîraqê
Serdema piştî Şerê Çaldiranê piraniya axên Kurdan êdî wek muttefîkê Osmaniyan ji alî mîrên Kurdan ve hatin rêvebirin. Tifaqa ku di navbera Kurdan û Yavuz Sultan Selîm de hatibû ava...
Bir Cumhuriyet Aydını: Cihad Baban’ın Gazeteciliği ve Siyasal Yaşamı
Bir Cumhuriyet Aydını: Cihad Baban’ın Gazeteciliği ve Siyasal Yaşamı
Irak’ın Süleymaniye şehri köklü ailelerinden Babanlar/Babanzadeler ailesinden gelen Cihad Baban, Cumhuriyet Dönemi’nde yetişmiş, önemli ve iz bırakan aydınlardan biridir. Mensubu b...
Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun
Makaɗan baka na Hausa sun karkasu dangane da rukunan mutanen da suke yi wa kiɗa da waƙa. Waɗannan rabe-rabe na makaɗan baka sun haɗa da makaɗan fada-wato waɗanda suke yi wa fadar s...

Back to Top