Javascript must be enabled to continue!
Dabarun Sata a Waƙoƙin Barayi na Kassu Zurmi:Koyar da Sata ko Ankararwa?
View through CrossRef
Waƙa ta baka ko rubutacciya, tamkar gyaɗa ce, sai an fasa akan san mai ƙwaya. Waƙoƙin ɓarayi da ake wa wani kallo na daban, su ma suna ɗauke da wani saƙo na musamman ta fuskar ankarar da jama’a irin dabarun da ɓarayi suke amfani da su wajen sata, domin jama’a su hankalta su kuma kiyaye. Wannan takarda da aka wa taken “Dabarun Sata a Waƙoƙin Ɓarayi na Kassu Zurmi: Koyar da Sata ko Ankararwa? Takarda ce da ta yi nazarin wasu waƙoƙin ɓarayi na Kassu Zurmi guda biyu, domin fito da saƙon da waƙoƙin suke ɗauke da su na ankarar da jama’a dabarun sata da ɓarayi suke amfani da su. An yi amfani da rubutattun bayanai da sauraron waƙoƙin mawaƙin domin fito da misalai. A ƙarshen an gano cewa akwai wasu lokuta da yanayi da ɓarayi suka fi so domin yin sata, wato kamar yanayi na damina da duhu, da kuma dare, sukan kuma yi sanɗa da dudduƙe domin kada motsin tafiyarsu ya tada mai gida.
Sokoto State University
Title: Dabarun Sata a Waƙoƙin Barayi na Kassu Zurmi:Koyar da Sata ko Ankararwa?
Description:
Waƙa ta baka ko rubutacciya, tamkar gyaɗa ce, sai an fasa akan san mai ƙwaya.
Waƙoƙin ɓarayi da ake wa wani kallo na daban, su ma suna ɗauke da wani saƙo na musamman ta fuskar ankarar da jama’a irin dabarun da ɓarayi suke amfani da su wajen sata, domin jama’a su hankalta su kuma kiyaye.
Wannan takarda da aka wa taken “Dabarun Sata a Waƙoƙin Ɓarayi na Kassu Zurmi: Koyar da Sata ko Ankararwa? Takarda ce da ta yi nazarin wasu waƙoƙin ɓarayi na Kassu Zurmi guda biyu, domin fito da saƙon da waƙoƙin suke ɗauke da su na ankarar da jama’a dabarun sata da ɓarayi suke amfani da su.
An yi amfani da rubutattun bayanai da sauraron waƙoƙin mawaƙin domin fito da misalai.
A ƙarshen an gano cewa akwai wasu lokuta da yanayi da ɓarayi suka fi so domin yin sata, wato kamar yanayi na damina da duhu, da kuma dare, sukan kuma yi sanɗa da dudduƙe domin kada motsin tafiyarsu ya tada mai gida.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Dabarun Jan Hankali A Waƙoƙin Baka: Nazari A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Dabarun Jan Hankali A Waƙoƙin Baka: Nazari A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Waƙoƙin baka na Hausa cike suke da dabarun jawo hankali. Wannan ya sa a kodayaushe za a ga waƙoƙin suna cike da armashi da salo mai ban-sha'awa. Gusau (2003 da 2023) ya kir...
Tasirin Zuga a Wasu Waƙoƙin Maƙaɗa Kassu Zurmi
Tasirin Zuga a Wasu Waƙoƙin Maƙaɗa Kassu Zurmi
Waƙa ta baka ko rubutacciya, tamkar gyaɗa ce, sai an fasa akan san mai ƙwaya. Waƙoƙin ɓarayi da ake wa wani kallo na daban, su ma suna ɗauke da wani saƙo na musamman ta fuskar anka...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Yanaye-Yanayen Sata: Nazari Daga Wasu Wakoki na Kassu Zurmi
Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuri’arsa abin faɗi d...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

