Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Tasirin Zuga a Wasu Waƙoƙin Maƙaɗa Kassu Zurmi

View through CrossRef
Waƙa ta baka ko rubutacciya, tamkar gyaɗa ce, sai an fasa akan san mai ƙwaya. Waƙoƙin ɓarayi da ake wa wani kallo na daban, su ma suna ɗauke da wani saƙo na musamman ta fuskar ankarar da jama’a irin dabarun da ɓarayi suke amfani da su wajen sata, domin jama’a su hankalta su kuma kiyaye. Wannan takarda da aka wa taken “Dabarun Sata a Waƙoƙin Ɓarayi na Kassu Zurmi: Koyar da Sata ko Ankararwa? Takarda ce da ta yi nazarin wasu waƙoƙin ɓarayi na Kassu Zurmi guda biyu, domin fito da saƙon da waƙoƙin suke ɗauke da su na ankarar da jama’a dabarun sata da ɓarayi suke amfani da su. An yi amfani da rubutattun bayanai da sauraron waƙoƙin mawaƙin domin fito da misalai. A ƙarshen an gano cewa akwai wasu lokuta da yanayi da ɓarayi suka fi so domin yin sata, wato kamar yanayi na damina da duhu, da kuma dare, sukan kuma yi sanɗa da dudduƙe domin kada motsin tafiyarsu ya tada mai gida.
Title: Tasirin Zuga a Wasu Waƙoƙin Maƙaɗa Kassu Zurmi
Description:
Waƙa ta baka ko rubutacciya, tamkar gyaɗa ce, sai an fasa akan san mai ƙwaya.
Waƙoƙin ɓarayi da ake wa wani kallo na daban, su ma suna ɗauke da wani saƙo na musamman ta fuskar ankarar da jama’a irin dabarun da ɓarayi suke amfani da su wajen sata, domin jama’a su hankalta su kuma kiyaye.
Wannan takarda da aka wa taken “Dabarun Sata a Waƙoƙin Ɓarayi na Kassu Zurmi: Koyar da Sata ko Ankararwa? Takarda ce da ta yi nazarin wasu waƙoƙin ɓarayi na Kassu Zurmi guda biyu, domin fito da saƙon da waƙoƙin suke ɗauke da su na ankarar da jama’a dabarun sata da ɓarayi suke amfani da su.
An yi amfani da rubutattun bayanai da sauraron waƙoƙin mawaƙin domin fito da misalai.
A ƙarshen an gano cewa akwai wasu lokuta da yanayi da ɓarayi suka fi so domin yin sata, wato kamar yanayi na damina da duhu, da kuma dare, sukan kuma yi sanɗa da dudduƙe domin kada motsin tafiyarsu ya tada mai gida.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Zuga A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Zuga A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Zuga wata hanya ce da mawaƙa suke amfani da ita domin karsashi ko ƙwazo na abin da ake son ya aikata. Mawaƙa na amfani da wannan salo a cikin waƙa domin su wasa su kuma zuga wanda ...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Nazarin Sigogin Zuga A Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Nazarin Sigogin Zuga A Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
An lura cewa manufar wannan takarda shi ne yin nazarin zuga daga cikin wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurma da kuma irin tasirin da zugan yake da shi a waƙar. Inda ƙarshen taka...

Back to Top