Javascript must be enabled to continue!
Zuga A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Zuga wata hanya ce da mawaƙa suke amfani da ita domin karsashi ko ƙwazo na abin da ake son ya aikata. Mawaƙa na amfani da wannan salo a cikin waƙa domin su wasa su kuma zuga wanda suke yi wa waƙa. Kasancewar Kassu makaɗin maza, dole ne ya yi amfani da salon zuga domin ya kwarzanta mutanensa. A wannan muƙala, an kawo ma’anar zuga da ire-iren waƙoƙin Kassu Zurmi waɗanda ake samun zuga a cikinsu. An kuma kawo misalan waƙoƙin Kassu Zurmi guda takwas tare da kawo inda aka sami zuga a cikinsu. Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan muƙal shi ne ta hanyar sauraren waƙoƙi a MP da wayar salula da kuma littattafai da aka wallafa a kan Kassu Zurmi.
Sokoto State University
Title: Zuga A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Zuga wata hanya ce da mawaƙa suke amfani da ita domin karsashi ko ƙwazo na abin da ake son ya aikata.
Mawaƙa na amfani da wannan salo a cikin waƙa domin su wasa su kuma zuga wanda suke yi wa waƙa.
Kasancewar Kassu makaɗin maza, dole ne ya yi amfani da salon zuga domin ya kwarzanta mutanensa.
A wannan muƙala, an kawo ma’anar zuga da ire-iren waƙoƙin Kassu Zurmi waɗanda ake samun zuga a cikinsu.
An kuma kawo misalan waƙoƙin Kassu Zurmi guda takwas tare da kawo inda aka sami zuga a cikinsu.
Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan muƙal shi ne ta hanyar sauraren waƙoƙi a MP da wayar salula da kuma littattafai da aka wallafa a kan Kassu Zurmi.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Tarken Yabo da Zuga a cikin wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Yabo a fagen waƙa wasu kalamai ne da ake yi domin faranta ran wanda ake yi wa waƙa. Zuga kuma ita ce ingiza ko kwarzanta wanda ake yabawa a cikin waƙa. Makaɗa Sa'idu Faru fitaccen ...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Salon Labartawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fa...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...

