Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

NAZARIN MA’ANA A KALAMAN KASSU ZURMI A CIKIN WASU WAƘOƘINSA

View through CrossRef
Wannan maƙala tana bincike ne a kan ma’anar wasu kalaman da Kassu Zurmi ya yi amfani da su a waƙoƙinsa domin ya fito da ma’anar abin da yake magana a kan sa. A wannan nazari an yi amfani da ra’in aiwatarwa. Kuma an tattara bayanan wannan maƙala daga waƙoƙin Kassu Zurmi da littattafan ilimin ma’ana da kuma ƙamusoshin Hausa. A cikin wannan maƙala an kawo matsayin kalma ko jimla a ilimin ma’ana tare da bayanin ma’anarta. A ƙarshen wannan binciken an gano matsayi da ma’anonin kalamai da yawa na Kassu Zurmi a waƙoƙinsa daban-daban. Kamar ma’ana ‘Ɗa’ tana iya ɗaukar ma’anoni irin wanda aka haifa namiji, wanda ba bawa ba, mutum mai mutunci da sauransu. Wannan bincike gudummuwa ce ga koyo da koyarwa a harshen Hausa.
Title: NAZARIN MA’ANA A KALAMAN KASSU ZURMI A CIKIN WASU WAƘOƘINSA
Description:
Wannan maƙala tana bincike ne a kan ma’anar wasu kalaman da Kassu Zurmi ya yi amfani da su a waƙoƙinsa domin ya fito da ma’anar abin da yake magana a kan sa.
A wannan nazari an yi amfani da ra’in aiwatarwa.
Kuma an tattara bayanan wannan maƙala daga waƙoƙin Kassu Zurmi da littattafan ilimin ma’ana da kuma ƙamusoshin Hausa.
A cikin wannan maƙala an kawo matsayin kalma ko jimla a ilimin ma’ana tare da bayanin ma’anarta.
A ƙarshen wannan binciken an gano matsayi da ma’anonin kalamai da yawa na Kassu Zurmi a waƙoƙinsa daban-daban.
Kamar ma’ana ‘Ɗa’ tana iya ɗaukar ma’anoni irin wanda aka haifa namiji, wanda ba bawa ba, mutum mai mutunci da sauransu.
Wannan bincike gudummuwa ce ga koyo da koyarwa a harshen Hausa.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Makaɗa suna amfani da wani nao’in salo da ake kira salon dibilwa, a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani salo ne na nuna gwanintar harshe da ƙwarewa ta yadda sukan kawo wata kalma da a...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
Faɗi-Tashin Auren Bahaushe:Nazari daga waƙar kassu zurmi ta shayi ɗangidan labbo
A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya...
KALAMAN GASKIYA DA ƘIRƘIRA A BAKIN KASSU ZURMI: NAZARI DAGA WASU WAƘOƘINSA
KALAMAN GASKIYA DA ƘIRƘIRA A BAKIN KASSU ZURMI: NAZARI DAGA WASU WAƘOƘINSA
Wannan maƙala mai taken Kalaman Gaskiya da na Ƙirƙira a Bakin Kassu Zurmi Nazari Daga wasu Waƙoƙinsa: Ta Kalli irin yadda Kassu ke fitowa da mazaunin gaskiya da yadda yake furta wa...
Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wannan takarda mai taken “Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” ta yi sharhin aikatau dangane da abin da ya shafi giredi, musamman dangane da Hausar Yamma. Harshen Hau...

Back to Top