Javascript must be enabled to continue!
Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Wannan takarda mai taken “Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” ta yi sharhin aikatau dangane da abin da ya shafi giredi, musamman dangane da Hausar Yamma. Harshen Hausa kamar wasu harsunan duniya, shi ma yana ɗauke da ajin aikatau a cikin sa. Manufar wannan takarda ita ce fito da kuma yin nazarin wasu kalmomin aikatau da makaɗa Kassu Zumi ya yi amfani da su a cikin wasu daga cikin waƙoƙinsa, domin aza su bisa ga sikeli a ga wane giredi za su iya hawa da wanda ba za su iya hawa ba. An yi amfani da hanyar sauraren waƙoƙin ne kamar sau biyu ko uku ko ma fiye da haka a wani lokaci domin a fitar da nau’o’in aikatau da ake nema tare da karanta littattafan da aka rubuta waƙoƙin. An yi amfani da hanyar bayanin aikatau da F.W Parsons ya assasa a shekarar 1960, wanda Amfani ya faɗaɗa a 1995 da 2005. Wannan takarda ta gano kusan dukkan aikatau sha-rinjaye da aka yi amfani da su masu gaɓa biyu ko uku suna iya ɗaukar mafi yawa giredin ko darajojin nan guda bakwai, amma za a yi amfani da aikatau mai gaɓa bibbiyu, musamman wanda ya shafi giredi na biyar domin ganin yadda suka bayyana a Hausar Yamma.
Sokoto State University
Title: Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Wannan takarda mai taken “Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” ta yi sharhin aikatau dangane da abin da ya shafi giredi, musamman dangane da Hausar Yamma.
Harshen Hausa kamar wasu harsunan duniya, shi ma yana ɗauke da ajin aikatau a cikin sa.
Manufar wannan takarda ita ce fito da kuma yin nazarin wasu kalmomin aikatau da makaɗa Kassu Zumi ya yi amfani da su a cikin wasu daga cikin waƙoƙinsa, domin aza su bisa ga sikeli a ga wane giredi za su iya hawa da wanda ba za su iya hawa ba.
An yi amfani da hanyar sauraren waƙoƙin ne kamar sau biyu ko uku ko ma fiye da haka a wani lokaci domin a fitar da nau’o’in aikatau da ake nema tare da karanta littattafan da aka rubuta waƙoƙin.
An yi amfani da hanyar bayanin aikatau da F.
W Parsons ya assasa a shekarar 1960, wanda Amfani ya faɗaɗa a 1995 da 2005.
Wannan takarda ta gano kusan dukkan aikatau sha-rinjaye da aka yi amfani da su masu gaɓa biyu ko uku suna iya ɗaukar mafi yawa giredin ko darajojin nan guda bakwai, amma za a yi amfani da aikatau mai gaɓa bibbiyu, musamman wanda ya shafi giredi na biyar domin ganin yadda suka bayyana a Hausar Yamma.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...