Javascript must be enabled to continue!
Habaici a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
View through CrossRef
Waƙawani ɓangare ne na adabin Hausa wadda kuma hanya ce da akan yi amfani da ita wajen gina tunanin al’umma da fahimtar da su wasu hanyoyin gudanar da rayuwarsu. Dabarun isar da saƙonni ta hanyar amfani da waƙa suna da matuƙar yawan gaske. Wannan shi ya samawa ƙasukanyi amfani da hanyoyi iri daban-daban domin isar da saƙonninsu. Wannan maƙalar za ta kalli waƙoƙin makaɗin nan mai suna Kassu Zurmi, da irin yadda yakan yi amfani da habaici wajen gabatar da waƙoƙinsa. Kyakkyawan nazari da sauraron waƙoƙinsa su ne hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan maƙalar. Sannan kuma an yi amfani da ra’i wanda yake nuni da yadda akan yi amfani da adabi ko al’ada ko harshe a matsayin madubi ko kyallaro al’adun al’umma kamar yadda Ado (2017:87) ya bayyana wajen gudanar da maƙalar. A ƙarshen wannan maƙalar, za a fahimci cewa mawaƙi Kassu Zurmi ya ƙware matuƙa wajen amfani da habaici a cikin waƙoƙinsa wanda wani ɓangare ne na adabin Hausa.
Sokoto State University
Title: Habaici a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Description:
Waƙawani ɓangare ne na adabin Hausa wadda kuma hanya ce da akan yi amfani da ita wajen gina tunanin al’umma da fahimtar da su wasu hanyoyin gudanar da rayuwarsu.
Dabarun isar da saƙonni ta hanyar amfani da waƙa suna da matuƙar yawan gaske.
Wannan shi ya samawa ƙasukanyi amfani da hanyoyi iri daban-daban domin isar da saƙonninsu.
Wannan maƙalar za ta kalli waƙoƙin makaɗin nan mai suna Kassu Zurmi, da irin yadda yakan yi amfani da habaici wajen gabatar da waƙoƙinsa.
Kyakkyawan nazari da sauraron waƙoƙinsa su ne hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan maƙalar.
Sannan kuma an yi amfani da ra’i wanda yake nuni da yadda akan yi amfani da adabi ko al’ada ko harshe a matsayin madubi ko kyallaro al’adun al’umma kamar yadda Ado (2017:87) ya bayyana wajen gudanar da maƙalar.
A ƙarshen wannan maƙalar, za a fahimci cewa mawaƙi Kassu Zurmi ya ƙware matuƙa wajen amfani da habaici a cikin waƙoƙinsa wanda wani ɓangare ne na adabin Hausa.
Related Results
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure
Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi
An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa al’adar Tauri...
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Al’adun kyautata zamantakewa, al’adu ne masu ɗimbin yawa da har yau ba a ƙayyade su ba, da ma dai al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Don haka dukkan tsarin da al’ad...
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Salon Dibilwa da Azancin Magana a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi
Makaɗa suna amfani da wani nao’in salo da ake kira salon dibilwa, a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani salo ne na nuna gwanintar harshe da ƙwarewa ta yadda sukan kawo wata kalma da a...
Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wannan takarda mai taken “Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” ta yi sharhin aikatau dangane da abin da ya shafi giredi, musamman dangane da Hausar Yamma. Harshen Hau...
NAZARIN ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
NAZARIN ADON HARSHE A WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Manufar wannan takarda ita ce zaƙulo irin fasahar da hikimar da Allah ya yi wa makaɗa Kassu Zurmi a fagen waƙa, tare da bayyana irin yadda yake amfani da nau’o’in Adon harshe daban...

