Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Ɗarsashin Zuci a Cikin Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

View through CrossRef
Wannan takarda ta ƙunshi tsokaci ne, ko nazari kan yadda Aminu Ladan Abubakar ALA ya sarrafa wasu zantuttuka da kalmomi masu alaƙa da ɗarsashin zuci cikin wasu waƙoƙinsa. Mawaƙin ya sarrafa zantuttuka da dama, domin faɗakarwa da ilmantarwa ko wa’azantarwa a kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum. Batutuwa masu alaƙa da ɗarsashin zuciya, batutuwa ne da suka faru ba wai shaci faɗi ba, waɗanda suke sosa zuciyar mawaƙin a duk lokacin da suka faɗo masa rai, ko suka motsa masa zuciya. Har wa yau kuma batutuwa ne da suke riƙe a zuciyar mawaƙin yake ganin ba zai iya mantawa da su ba a rayuwa. A taƙaice dai manufar wannan nazari shi ne fito da tasiri da muhimmancin ire-iren waɗannan zantuttuka da kalmomi, waɗanda mawaƙin ya sarrafa a cikin waƙoƙinsa. An yi amfani da ɗiyoyin waƙoƙin mawaƙin a inda aka tattara bayani da suka shafi ɗarsuwan zuci, wanda a ƙarshen binciken an gano cewa sarrafa ire-iren waɗannan zantattuka masu alaƙa da ɗarsashin zuci a waƙa, suna da tasiri da muhimmanci domin kusan duk abubuwan da mawaƙin yake ambatawa a waƙar, tabbatattu ne wato sun faru a zahirance, ba wani shaci faɗi ba ne..
SASPR Edu International Pvt. Ltd
Title: Ɗarsashin Zuci a Cikin Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)
Description:
Wannan takarda ta ƙunshi tsokaci ne, ko nazari kan yadda Aminu Ladan Abubakar ALA ya sarrafa wasu zantuttuka da kalmomi masu alaƙa da ɗarsashin zuci cikin wasu waƙoƙinsa.
Mawaƙin ya sarrafa zantuttuka da dama, domin faɗakarwa da ilmantarwa ko wa’azantarwa a kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum.
Batutuwa masu alaƙa da ɗarsashin zuciya, batutuwa ne da suka faru ba wai shaci faɗi ba, waɗanda suke sosa zuciyar mawaƙin a duk lokacin da suka faɗo masa rai, ko suka motsa masa zuciya.
Har wa yau kuma batutuwa ne da suke riƙe a zuciyar mawaƙin yake ganin ba zai iya mantawa da su ba a rayuwa.
A taƙaice dai manufar wannan nazari shi ne fito da tasiri da muhimmancin ire-iren waɗannan zantuttuka da kalmomi, waɗanda mawaƙin ya sarrafa a cikin waƙoƙinsa.
An yi amfani da ɗiyoyin waƙoƙin mawaƙin a inda aka tattara bayani da suka shafi ɗarsuwan zuci, wanda a ƙarshen binciken an gano cewa sarrafa ire-iren waɗannan zantattuka masu alaƙa da ɗarsashin zuci a waƙa, suna da tasiri da muhimmanci domin kusan duk abubuwan da mawaƙin yake ambatawa a waƙar, tabbatattu ne wato sun faru a zahirance, ba wani shaci faɗi ba ne.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Nazarin Fanɗararrun Zantuka a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi
Nazarin Fanɗararrun Zantuka a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi
Manufar wannan takarda ita ce yin ninƙaya cikin waƙoƙin Abubakar Kassu domin fito da wasu zantuka waɗanda suka ci karo da addini ko al’ada kamar yadda suka wanzu a waƙoƙin makaɗin....
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
A kowane lokaci adabin al’uma kan fayyace yadda rayuwa da tsarin zamantakewar al’umar ke wakana ne, ta yadda ake sa rai idan an dubi adabin wannnan al’umar a iya hango hoton rayuwa...
Mabuɗin Turken Ɗarsashin Zuciya: Keɓaɓɓen Nazari Kan Mabuɗin Turken Ɗarsashin Zuciya a wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Garba Maitandu
Mabuɗin Turken Ɗarsashin Zuciya: Keɓaɓɓen Nazari Kan Mabuɗin Turken Ɗarsashin Zuciya a wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Garba Maitandu
Waƙoƙin ɗarsashi ko rinjayen zuciya, waƙoƙi ne da kan wanzu a sakamakon wani abu da ya motsa wa mutum rai, da ya danganci farin ciki, ko farin rai, ko akasin haka, wato bakin ciki....
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Gurbin Waƙoƙin Yara Mata da ‘Yammata a Rayuwar Hausawa
Waƙoƙin yara mata da ‘yammata wani babban rukuni ne a al’adar Hausawa. Waƙoƙi ne da ake yi domin samun nishaɗi da tarbiyya da ilmantarwa da kuma gargaɗi ga ‘yammata tun suna ƙanana...
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka
Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago s...

Back to Top