Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

NAZARIN JIMLOLIN TAMBAYA A CIKIN WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI

View through CrossRef
Mawaƙan Hausa mutane ne da Allah ya ba su hikima da baiwa ta wani muhimmin runbun adana tarihi da bunƙasa harshe da al’adu da adabin Hausa. Hakan ya sa ake samun abubuwa da yawa masu muhimmanci a waƙoƙinsu. Manufar wannan maƙala ita ce nazarin jumlolin tambaya a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi. Kasancewar duk maganar da ɗan adam ke furtawa sautuka ne ake harhaɗawa, a samu gaɓa, a haɗa gaɓoɓin a samar da kalma, a haɗa kalmomin a samar da jumloli a harshe. Masana nazari harshe sun rarraba jumlolin Hausa ko dai ta fuskar tsarin jumlolin ko kuma ta fuskar aikinsu, a wannan takarda za a dubi nau’o’in jumloli ta fuskar aikinsu, amma wannan takarda za ta mayar da hankali kan jumlolin tambaya da Kassu ya yi amfani da su a cikin wasu waƙoƙinsa da maƙasudin yin tambayar, kamar tambaya ta sigar roƙo ko tambaya ta sigar ƙalubalanta da ta gwarzantawa da kuma ta fuskar kiranye. Wannan takarda ta gano cewa a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi akwai ɗinbin jumlolin tambaya ko masu sigar tambaya cikinsu. Don haka ne wannan takardar ta taskace wasu daga ciki, kuma ta yi cikakken sharhi a kan su.
Title: NAZARIN JIMLOLIN TAMBAYA A CIKIN WASU WAƘOƘIN KASSU ZURMI
Description:
Mawaƙan Hausa mutane ne da Allah ya ba su hikima da baiwa ta wani muhimmin runbun adana tarihi da bunƙasa harshe da al’adu da adabin Hausa.
Hakan ya sa ake samun abubuwa da yawa masu muhimmanci a waƙoƙinsu.
Manufar wannan maƙala ita ce nazarin jumlolin tambaya a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi.
Kasancewar duk maganar da ɗan adam ke furtawa sautuka ne ake harhaɗawa, a samu gaɓa, a haɗa gaɓoɓin a samar da kalma, a haɗa kalmomin a samar da jumloli a harshe.
Masana nazari harshe sun rarraba jumlolin Hausa ko dai ta fuskar tsarin jumlolin ko kuma ta fuskar aikinsu, a wannan takarda za a dubi nau’o’in jumloli ta fuskar aikinsu, amma wannan takarda za ta mayar da hankali kan jumlolin tambaya da Kassu ya yi amfani da su a cikin wasu waƙoƙinsa da maƙasudin yin tambayar, kamar tambaya ta sigar roƙo ko tambaya ta sigar ƙalubalanta da ta gwarzantawa da kuma ta fuskar kiranye.
Wannan takarda ta gano cewa a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi akwai ɗinbin jumlolin tambaya ko masu sigar tambaya cikinsu.
Don haka ne wannan takardar ta taskace wasu daga ciki, kuma ta yi cikakken sharhi a kan su.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Na...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Lokutan Gargajiya Dana Addini A Bakin Kassu Zurmi
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a w...

Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...

Back to Top