Search engine for discovering works of Art, research articles, and books related to Art and Culture
ShareThis
Javascript must be enabled to continue!

Yanayin Halayen Duniya a Wasu Waƙoƙin Adamu Ɗanmaraya Jos

View through CrossRef
Wannan maƙala ta gudana ne a kan wasu waƙoƙin makaɗa Adamu Ɗanmaraya Jos, wanda ya kasance makaɗi ne mai ɗabbaƙa al’adun al’ummarsa da kuma bibiyar yanayin rayuwarsu, da kuma irin yadda suke gudanar da ita a cikin duniya. Manufar wannan takarda ita ce fito da wasu halaye da yanayi na rayuwar duniya a zubin ɗiyan waƙoƙin Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos. A yawancin waƙoƙinsa ya kan fito da saƙonni waɗanda suka dace da halayen rayuwar duniya ta nuna yadda zamantakewar al’umma ta ke. Wannan bincike an tsara shi ne bisa ra’in tsarin al’adu, wato, Cultural Schema Theory. An ƙirƙiri wannan ra'in ne a ƙarshen shekarar 1980s, waɗanda suka fara amfani da shi su ne, Naomi Quinn da masanin halayyar ɗan'adam Claudia Strauss. Ra’in ya bayyana cewa ana nazartar zamantakewar rayuwa da tunanin ɗan’adam a maganganunsa ko a cikin adabin da ya samar. Hakan ya sa aka yi amfani da wannan ra’i wajen nazartar tunanin Adamu Ɗanmaraya Jos game da duniya. Nazarin ya kafa hujja daga wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗin. Masana sun yi amfani da wannan ra’in wajen binciken tunanin mutane, musamman a fannin adabi irin su Kennedy (1994) da Pedersen (1994) da Houghton (2012) da sauransu. Haka kuma, an nemo misalan waƙoƙin ne daga kafar intanet da amfani da Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa Gusau, (2019). A wannan maƙala an fahimci irin yadda Ɗanmaraya Jos ya fito da halin duniya da yanayin da take sanya mutane, musamman waɗanda suka ruɗu da ita, da kuma irin sauyin da ta ke yi wa mutane na ɗauka da ajiyewa. Har ila yau kuma, mawaƙin ya fayyace irin yadda duniya ta kasance mayaudariya, wadda ba ta da gwani. Haka kuma, an nuna cewa komai na duniya samamme ne kuma ƙararre, saboda haka duk abin da ke cikin duniya yana da lokaci, wata rana zai zama tarihi.
Title: Yanayin Halayen Duniya a Wasu Waƙoƙin Adamu Ɗanmaraya Jos
Description:
Wannan maƙala ta gudana ne a kan wasu waƙoƙin makaɗa Adamu Ɗanmaraya Jos, wanda ya kasance makaɗi ne mai ɗabbaƙa al’adun al’ummarsa da kuma bibiyar yanayin rayuwarsu, da kuma irin yadda suke gudanar da ita a cikin duniya.
Manufar wannan takarda ita ce fito da wasu halaye da yanayi na rayuwar duniya a zubin ɗiyan waƙoƙin Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos.
A yawancin waƙoƙinsa ya kan fito da saƙonni waɗanda suka dace da halayen rayuwar duniya ta nuna yadda zamantakewar al’umma ta ke.
Wannan bincike an tsara shi ne bisa ra’in tsarin al’adu, wato, Cultural Schema Theory.
An ƙirƙiri wannan ra'in ne a ƙarshen shekarar 1980s, waɗanda suka fara amfani da shi su ne, Naomi Quinn da masanin halayyar ɗan'adam Claudia Strauss.
Ra’in ya bayyana cewa ana nazartar zamantakewar rayuwa da tunanin ɗan’adam a maganganunsa ko a cikin adabin da ya samar.
Hakan ya sa aka yi amfani da wannan ra’i wajen nazartar tunanin Adamu Ɗanmaraya Jos game da duniya.
Nazarin ya kafa hujja daga wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗin.
Masana sun yi amfani da wannan ra’in wajen binciken tunanin mutane, musamman a fannin adabi irin su Kennedy (1994) da Pedersen (1994) da Houghton (2012) da sauransu.
Haka kuma, an nemo misalan waƙoƙin ne daga kafar intanet da amfani da Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa Gusau, (2019).
A wannan maƙala an fahimci irin yadda Ɗanmaraya Jos ya fito da halin duniya da yanayin da take sanya mutane, musamman waɗanda suka ruɗu da ita, da kuma irin sauyin da ta ke yi wa mutane na ɗauka da ajiyewa.
Har ila yau kuma, mawaƙin ya fayyace irin yadda duniya ta kasance mayaudariya, wadda ba ta da gwani.
Haka kuma, an nuna cewa komai na duniya samamme ne kuma ƙararre, saboda haka duk abin da ke cikin duniya yana da lokaci, wata rana zai zama tarihi.

Related Results

Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nazarin Sunaye A Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masan...
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Dangantakar ‘Yantauri Da Sarauta A Zamantakewar Hausawa: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zaman...
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Wando Sai Da Zariya: Ƙimar Namiji A Wajen Mace A Mahangar Kassu Zurmi
Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsari...
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Wasu Ɓoyayyin Taurari a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo...
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da ...
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
Salon Hira a Cikin Waƙar Nomau Namagarya da Waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo ta Kassu Zurmi
An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunaw...
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Salon Jerin Sarƙe a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Masana sun tabbatar da cewa, Salo ya ƙunshi duk wasu dabaru da hikimomin jawo hankali domin a isar da saƙo cikin harshe mai burgewa da saka karsashi da kuma jawo hankali ga mai sau...
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Nason Wasu Al’adun Kyautata Zamantakewar Hausawa A Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi
Al’adun kyautata zamantakewa, al’adu ne masu ɗimbin yawa da har yau ba a ƙayyade su ba, da ma dai al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Don haka dukkan tsarin da al’ad...

Back to Top